An Kama Dan Bindiga da Kayan Soji, Asirin Masu Safarar Makamai Ya Tonu a Filato

An Kama Dan Bindiga da Kayan Soji, Asirin Masu Safarar Makamai Ya Tonu a Filato

  • Sojojin Runduna ta 3 tare da Operation Safe Haven sun cafke wani da ake zargi ɗan bindiga ne a Zangon Kataf, Jihar Kaduna
  • An kama shi ne yayin da yake sanye da kayan sojoji yana ƙoƙarin yin garkuwa ko fashi da makami a cikin al’umma
  • Haka nan a wani samame daban a Filato, an gano ɗakunan ajiye makamai da harsasai da kuma babur da aka bari aka gudu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Rundunar sojoji a ƙarƙashin Operation Safe Haven tare da runduna ta 3 ta samu nasarar cafke wani ɗan bindiga yayin da ya ke sanye da kayan sojoji.

Baya ga haka, rundunar ta yi nasarar gano wata maboyar makamai a wani samame da ta kai a jihar Filato.

Wanda aka kama a Kaduna
Wanda aka kama da kayan soji a Kaduna. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Facebook

Bayanan tsaro da Zagazola Makama ya wallafa a X sun nuna cewa samamen na Kaduna da Filato ya kawo wani ci gaba a yaki da miyagun laifuffuka a Arewa ta Tsakiyar ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce an kama mutumin a Katsit, karamar hukumar Zangon Kataf, inda ake zargin yana kwaikwayon sojoji don yaudara da fashi a cikin al’umma.

An kama mai saka kayan sojoji da bindiga

Rahotanni sun nuna cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 15 ga Yuni, a Katsit cikin Jihar Kaduna, mutumin dai na sanye da kayan yaƙi irin na soja yayin da jami’an tsaro suka tare shi.

Bincike ya gano cewa an samu bindigar AK-47 a hannunsa, harsasai guda uku, ƙananan harsasai guda bakwai, kati na bogi na rundunar ‘yan banga, waya da kuma kati na ATM guda biyu.

The Guardian ta rahoto cewa mutumin yana hannun jami’an tsaro a yanzu haka domin zurfafa bincike da shirin daukar matakin doka a kan shi.

An gano bindigogi da harsasai a Filato

A wani samame daban da aka kai a Kwanar Lauje cikin karamar hukumar Bassa ta Jihar Filato, sojoji sun mamaye wani wuri da ake zargin maboyar masu safarar makamai ce.

Bayan isarsu, wadanda ake zargi sun tsere, amma jami’an tsaron sun gudanar da bincike inda suka gano bindiga AK-47, harsasai 300, da wasu na'ukan harsasai.

Har ila yau, sojoji sun kwato wata babur da mutanen da ake zargin suka bari yayin da suka gudu daga wajen.

Sojoji za su cigaba da farautar 'yan bindiga
Sojoji za su cigaba da farautar 'yan bindiga. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Sojoji na ci gaba da farautar barayin

Rahotanni sun bayyana cewa dukkan kayan da aka gano yanzu haka na hannun jami’an tsaro yayin da ake cigaba da gudanar da samame don kama wadanda suka tsere.

Wannan na daga cikin matakan da rundunar ke ɗauka don ƙarfafa tsaro da yaki da miyagun laifuffuka a yankunan da ke fama da matsalolin ‘yan bindiga da safarar makamai.

An yi Allah wadai da kisan Benue

A wani rahoton, kun ji cewa shugabanni da 'yan siyasa na cigaba da Allah wadai da kashe mutane a jihar Benue.

Rahotanni na nuni da cewa wasu 'yan ta'adda sun kai hari kan wasu kauyuka a jihar inda suka kashe mutane sama da 200.

Sanata Rabiu Kwankwaso, Sanata Abubakar Bukola Saraki da Sheikh Isa Ali Pantami sun yi Allah wadai da kisan da aka yi a Benue.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng