Hukumar NEMA
Hukumar NEMA ta ce mutum 236 sun mutu a ambaliyar ruwa da ta shafi jihohi 27 da Abuja, yayin da fiye da 400,000 suka rasa gidaje da gonaki a fadin kasa.
Ambaliya ta mamaye yankunan Ogidi da Ogbaru a Anambra bayan ruwan sama mai karfi, gidaje da gonaki sun nutse, gwamnati ta dauki matakan gaggawa don taimakawa jama’a.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA ta yi gargadin cewa ruwa zai iya kwararowa daga madatsun Kainji, Jebba, Shiroro da Zungeru da ke Neja.
Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa kan ambaliyar ruwa a wasu jihohi 14 da suka hada da Adamawa, Kebbi Sokoto da Legas. Ambaliya ta riga ta auku a Adamawa.
Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane 3 ciki har da mata biyu da namiji yayin da suke dawowa daga makaranta a Zariya, ana neman wata yarinya.
A labarin nan, za a ji yadda ruwa kamar da bakin kwarya a jihar Kaduna ya jefa bayin Allah a cikin wahala saboda rushewar muhallansu a sassa da dama.
Mummunar ambaliya ta mamaye kauyuka bakwai a Taraba bayan saukar ruwan sama mai yawa, inda kogin Benue ya yi ambaliya tare da lalata gidaje da gonaki.
Hukumar NEMA ta kai agajin gaggawa jihar Adamawa bayan ruwa ya jawo ambaliya a karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa. Gidaje da gonaki sun lalace.
Gwamnatin Najeriya ta samo tallafin Dala miliyan 1 daga kasar China domin raba wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa a Arewacin Najeriya a damunar bana.
Hukumar NEMA
Samu kari