Jirgin Sama Ya Sake Faduwa a Kasar India, an Rasa Rayukan Mutane 7 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya
- An kara samun sabon hatsarin jirgin sama a kasar India yayin da ake ciki gaba da jimamin mutuwar mutane sama da 270
- A makon jiya ne wani jirgi ya fadi a India, inda aka ce mutane sama da 200 sun mutu nan take bayan faduwarsa
- Haddura irin wadannan sun zama ruwan dare a duniya, kuma sukan faru tare da jawo mutuwar mutane da dama a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Uttarakhand, India - A yau Lahadi 15 ga watan Yunin 2025, wani jirgin sama mai saukar ungulu ya fado a wani yankin tsaunuka na jihar Uttarakhand da ke arewacin kasar India.
Wannan lamarin dai ya yi sanadin mutuwar duka mutane bakwai da ke cikin jirgin, ciki har da wata yarinya ‘yar shekara biyu.
Gwamnan jihar, Pushkar Singh Dhami, ya bayyana wannan labari a matsayin wani babban rashi mai tayar da hankali.

Asali: UGC
Halin da ake ciki bayan hatsarin
Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter), yana mai cewa tuni jami’an ceto da hukumomin yankin suka fara gudanar da ayyukan ceto da bincike a wurin da hatsarin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar gwamna Dhami:
“Labarin hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya faru a gundumar Rudraprayag abin bakin ciki ne kwarai. Mun tura jami’an SDRF da sauran hukumomin gaggawa zuwa wurin da hatsarin ya faru.”
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya tashi ne da misalin karfe 5:20 na safe agogon kasar India (kimanin karfe 11:50 na dare agogon GMT), yana kan tafiyar minti 10 kacal daga Shri Kedarnath Dham zuwa Guptkashi, kafin ya fado.
Hatsarin jirgin sama a India
Hatsarin ya faru ne kwana uku bayan wani babban hatsarin jirgin sama ya auku a birnin Ahmedabad inda wani jirgin fasinja ya fado cikin unguwa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 270.
Jami’an hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Uttarakhand (UCADA) sun ce jirgin ya kama da wuta bayan da ya fado, wanda hakan ya sa gawarwakin mutanen da ke ciki suka kone matuka, har da ta yarinyar da ke cikin jirgin.
Hukumar ta kuma bayyana cewa tuni an tura tawagar bincike zuwa wurin don gano musabbabin hatsarin.

Asali: Twitter
Halin da ake ciki a yankin
Wasu mazauna yankin da suka tafi daji domin yankan ciyawa ga dabbobinsu ne suka fara ganin guntun jirgin a cikin daji kuma suka sanar da jami’an tsaro, kamar yadda majiyar mujallar The Week ta ruwaito.
A halin yanzu, an killace yankin da hatsarin ya auku domin gudanar da bincike cikin tsanaki, yayin da jami’an ceto ke ci gaba da kokarin gano cikakken bayanin wadanda suka mutu da kuma nazarin dalilin fadowar jirgin.
Hatsari irin wannan ya zama ruwan dare a yankuna daban-daban na duniya, ciki har da nan gida Najeriya, inda ake samun haddura masu kai wa ga mutuwar jama’a.
Wani hatsarin a India
A wani labarin, sabon rahoto ya nuna cewa matuƙin jirgin Air India da ya yi hatsari a Ahmedabad ya aika da saƙo na gaggawa kafin hatsarin.
A cewar rahoton sadarwar rediyo ta ƙarshe da aka bayyana wa jama'a, matuƙin jirgin ya aika da kiran gaggawa (mayday), inda ya bayyana abin da ke faruwa a cikin jirgin.
A cikin kalamansa na ƙarshe, matuƙin jirgin, Kyaftin Sumeet Sabharwal, ya bayyana sarai cewa jirgin Boeing 787-8 Dreamliner ya gaza samun ƙarfin tashi, inji rahoton The Sun.
Asali: Legit.ng