Zanga Zanga Ta Barke a Benue kan Rashin Tsaro, an Samu Bayanai
- Yawan hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa a jihar Benue sun sanya matasa sun fito kan tituna domin nuna rashin amincewarsu
- Matasan masu yawa sun fito kan tituna domin nuna rashin gamsuwarsu kan yadda matsalar rashin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a jihar
- Zanga-zangar wacce aka fara da safiyar ranar Lahadi ta jawo cunkoson ababen hawa bayan da matasan suka mamaye tituna a birnin Makurdi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Wasu matasa masu yawa sun fito domin yin zanga-zangar lamuna a jihar Benue.
Matasan sun fito kan tituna ne kan don nuna rashin jin daɗi kan taɓarɓarewar tsaro da ya addabi jihar Benue.

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta rahoto cewa matasan sun fito ne da safiyar ranar Lahadi, 15 ga watan Yunin 2025 domin gudanar da zanga-zangar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasa sun fito kan tituna a Benue
Duk da tsauraran matakan tsaro da aka kafa a Makurdi, babban birnin jihar, matasan sun mamaye unguwar Wurukum da ke cikin birnin domin nuna damuwarsu kan yawaitar kashe-kashen da ake yi a faɗin jihar.
Sun yi watsi da gargaɗin gwamnatin jihar na gujewa tarukan da ba su da izini, inda suka buƙaci adalci da kuma ƙarfafa tsaro, suna zargin hukumomi da gazawa wajen kare rayukan mutanen da abin ya shafa a karkara.
Mafi yawan masu zanga-zangar sun sanya baƙaƙen kaya, tare da ɗauke da rassan dabino da alluna masu ɗauke da sakonni daban-daban na kiran kawo ƙarshen kashe-kashen, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Sun kuma toshe hanya mai yawan zirga-zirgar ababen hawa, inda suka hana motocin wucewa har sai buƙatunsu na tabbatar da tsaro da kare rayukan al'umma sun samu amsa.
Ƴan bindiga na kai hare-hare a Benue
Wannan zanga-zanga ta tayar da hankula a tsakanin direbobi da fasinjoji da ke kan titin, domin an hana su wucewa, lamarin da ya haddasa tsaiko da cunkoso a unguwar.
Zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da hare-haren da suka zama ruwan dare a jihar, wanda ke ci gaba da jefa rayukan al'umma cikin haɗari, musamman a ƙananan hukumomin Guma, Gwer ta Yamma, Apa da wasu sassa na jihar

Asali: Twitter
A ranar Asabar da ta gabata, wasu makiyaya masu dauke da makamai sun kai farmaki garuruwan Yelwata da Daudu a cikin Karamar Hukumar Guma, inda suka kashe ɗaruruwan mutane ciki har da jami’an tsaro.
Matasan sun bayyana cewa ba za su zauna shiru ba yayin da ake ci gaba da hallaka rayuka ba tare da matakin gaggawa daga gwamnati ba.
Gwamna Alia ya yi Allah wadai da harin ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi Allah wadai da harin da ƴan bindiga suka kai a jihar.
Gwamna Alia wanda ya nuna takaicinsa kan harin ya bayyana cewa rayukan ɗan Adam ba abin kashewa ba ne ba gaira ba dalili.
Hakazalika ya sha alwashin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba har sai ya tabbatar da zaman lafiya ya wanzu a jihar Benue.
Asali: Legit.ng