Ana Wata ga Wata: Gwamnatin Jigawa Ta Tsayar da Albashin Malaman Firamare 239
- Gwamnatin Jigawa ta rike albashin malamai 239 da aka gano sun yi watsi da aiki har tsawon shekaru, alhalin suna karbar albashi
- Hukumar SUBEB ta jihar ta bukaci wani malami da ya mayar wa gwamnati albashin shekaru uku da ya karba tun da bai yi aikin ba
- Shugaban SUBEB ya bukaci SBMC da sauran jama’a su taimaka wajen tona asirin malaman da ke sakaci da aikin koyarwa a makarantu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa – Hukumar ilimin bai daya ta jihar Jigawa ta yi babban gargadi ga malaman makarantun jihar game da rashin zuwa wurin aiki.
Domin nuna bacin ranta da kuma buga misali ga kafatanin malaman jihar, hukumar SUBEB ta rike albashin malamai 239 da aka gano sun yi watsi da ayyukansu.

Asali: Twitter
Dalilin tsayar da albashin malamai a Jigawa
Shugaban SUBEB, Farfesa Haruna Musa, ya bayana cewa an tsayar da albashin malamai 239 saboda rashin zuwa aiki na tsawon watanni zuwa shekaru uku, duk da suna karbar albashinsu, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Musa ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar, bayan kammala horo na kwanaki biyar ga malamai 250 da ke koyar da Larabci, da aka shirya a makarantar firamaren Takur da ke Dutse.
Ya bayyana cewa wasu malamai sun daina zuwa aji na tsawon lokaci duk da cewa gwamnati na ci gaba da biyansu albashi duk wata.
Wani malami zai dawo da albashin shekara 3
A misalin da aka buga, Haruna ya ambaci wani malamin firamare da a kwanan nan aka yi masa sarautar 'Mai Gari', wanda aka gano bai koyar da dalibai na tsawon shekaru uku ba.
Farfesa Haruna ya ce an umarci malamin da ya mayar wa gwamnatin Jigawa kudaden da ya karba ba tare da aiki ba, kuma ko da ya zabi ci gaba da aikin, sai ya biya bashin kudin.
Shugaban hukumar SUBEB ya kara da cewa wannan mataki wani bangare ne na yunkurin tabbatar da ingancin ilimi a jihar Jigawa.

Asali: Original
SUBEB ta horar da malamai kan ilimim kwamfuta
A cigaba da bayyana alkiblar SUBEB, Farfesa Haruna ya bukaci 'yan SBMC (kwamitin kula da hukumomin makarantu) da su taimaka wajen gano duk wani malami da yake sha-ruwan-tsuntsaye aikinsa, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a makarantu.
Ya ce hukumar SUBEB za ta ci gaba da daukar karin ma’aikata don cike gibi na karancin malamai da ake fsukanta a fadin jihar .
A bangare guda, Haruna ya bayyana cewa jami'o'in ilimi na Gumel da Babura sun horar da malamai kan ilimin na'ura mai kwakwalwa da yadda za su rika tsara jadawalin darussansu.
Shugaban hukumar ya bukaci malaman da ke koyar da Larabci da su riƙa saka tufafin da suka dace da amfani da harshe mai kyau yayin koyarwa, saboda dalibai na koyi da dabi'unsu.
An dauki malamai 5,000 aiki a Jigawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya sanar da ɗaukar sababbin malamai domin cike giɓin da ke akwai a ɓangaren ilimi a faɗin jihar.
Namadi ya ce ilimi na ɗaya daga cikin manyan manufofi 12 da gwamnatinsa ta sa a gaba, da nufin ɗaga darajar jihar tare da ƙara mata ɗaukaka a kowane fanni.
A cewar shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar (SUBEB), sababbin malaman da aka ɗauka su 5,000 sun shafe shekara biyu suna aikin wucin gadi kafin a ba su aikin din-din-din.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng