Za a dauki Malaman Makaranta 1, 736 a jihar Jigawa

Za a dauki Malaman Makaranta 1, 736 a jihar Jigawa

Za ku ji cewa gwamnatin jihar Jigawa za ta bayar da aiki ga Mutane 1, 736 domin koyarwa a Makarantun firamare da Sakandire na jihar.

A ranar Laraba ta yau din nan Alhaji Salisu Zakar, shugaban cibiyar ilimi na jihar watau SUBEB, ya bayyana hakan da cewar gwamnatin za ta debi malaman ne domin maganace karancin su musamman makarantu na firamare da kuma Sakandire dake jihar.

A yayin ganawa da manema labarai cikin babban birnin jihar na Dutse, Zakar ya bayyana cewa tuni gwamnatin ta dauki kimanin ma'aikata 868 cikin 1, 736 da ta kudirta bayan ta gudanar da gwaje-gwaje gami da jarrbawa kan mabukata aikin.

Za a dauki Malaman Makaranta 1, 736 a jihar Jigawa
Za a dauki Malaman Makaranta 1, 736 a jihar Jigawa

Legit.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu manema wannan aiki na zaman kiradadon sakamakon jarrabawar tantancewa da suka zana kamar yadda shugaban cibiyar ta SUBEB ya bayyana.

KARANTA KUMA: Ba bu ƙosawa amma na cancanci zama Shugaban 'Kasar Najeriya - Atiku

Zakar ya kara da cewa, sakamakon karancin malamai musamman a makarantun firamare da kuma na sakandire ya sanya gwamnan jihar, Muhammad Badaru Abubakar, ya gaggauta cike guraben malamai domin inganta harkokin ilimi.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin gwamnan Mallam Nasir El-Rufa'i, ta gudanar da makamancin wannan hobbasa domin bunkasa harkokin ilimi a jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng