'Ba Iyalan Aliero ba ne': Malami Ya Ƙaryata Labarin Cafke Matar Ɗan Bindiga a Saudiyya
- An ruwaito cewa an cafke wata mata da tsohuwa da ake zargin mahaifiyar Ado Aliero da matarsa ne a ƙasar Saudiyya
- Sheikh Musa Assadus Sunnah ya fito a bidiyo ya ƙaryata rahoton, yana mai cewa babu wata hujja da ke nuna suna da alaƙa da Aliero
- Ya ce kafafen sada zumunta ne suka yada hotunan mata da tsohuwa, ya koka kan rashin adalci da danganta laifi da waɗanda bai shafe su ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - A jiya Talata 20 ga watan Mayun 2027 aka ruwaito cewa an cafke wasu mata da ake zargin na da alaƙa da Ado Aliero.
Rahotanni sun ce an cafke mata da wata tsohuwa da ake zargin mahaifiyar Aliero ne da matarsa.

Asali: Facebook
Assadus Sunnah ya magantu kan kama iyalan Aleiro
Sheikh Musa Assadus Sunnah ya ƙaryata labarin a cikin faifan bidiyo da Mizani FM ta wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, malamin ya ce babu gaskiya kan cewa matan suna da alaka da fitaccen ɗan bindiga, Ado Aliero.
Ya koka kan yadda ake rashin adalci a cikin al'umma musamman danganta laifi da wadanda bai shafe su ba.
Ya ce:
"Dazu-dazu na ke cin karo da wasu rahotanni a kafofin yada labarai, an dauko hoton wata mata da wata tsohuwa an hada an ce mata da mahaifiyar Ado Aliero ne.
"Wai matarsa da mahaifiyarsa sun je aikin hajji an yi ram da su a kasar Saudiyya, wannan bidiyo ƙarya ne ba gaskiya ba ne.
"Duk wanda ka ga ya buga wannan a kowane gidan jarida karya ne, Ado Aliero bai da wata mata ko uwa da ta je aikin hajji."

Asali: Facebook
Sheikh Asadus Sunnah ya shawarci al'umma da adalci
Malamin ya ce idan aka yi rashin sa'a shikenan tsautsayi ya hau kan matan da aka kama wadanda watakila ba su san shi Ado Aliero ba a rayuwarsu.
Ya kara da cewa:
"Idan ba a yi sa'a ba, tsautsayi ne zai gitta kan wata mata, ai yan TikTok ne suka dauko hoton bafulatana suka hada aka ce ga matar Aliero.
"Idan ba sa'a ba kila ita da aka ɓatawa suna ba ta da alaka da shi ba ta ma san shi ba, ina suka hadu? Kawai don shi bafulatani ne ita ma haka.
"Mu ƙaddara ma mahaifiyarsa ce ko matarsa ce, shin a Musulunci da dokar kasa adalci ne don yana aikata laifi su suna da alaka da laifin."
Malamin ya nuna damuwa game da yadda laifin wani ke shafar wani wanda ya ce har a Musulunci hakan ba daidai ba ne.
Ya ba da misali kan abubuwan da ke faruwa na yan daba da cewa babu yadda za ka danganta iyayensu da laifin da suke aikatawa.
Ado Aliero ya kira taron gaggawa
A baya, kun ji cewa rikakken ɗan bindiga, Ado Aliero, ya kira taron gaggawa bayan kashe ɗan uwansa, Isuhu Yellow, da yaran Dogo Gide suka yi.
Wata majiya ta tabbatar da cewa an gudanar da taron ne a sansanin Aliero da ke dajin Munhaye, ƙaramar hukumar Tsafe a Zamfara.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa an ga ɗaruruwan ‘yan bindiga a babura suna tafiya zuwa Munhaye don halartar taron.
Asali: Legit.ng