Ana cikin Nemansa Ruwa a Jallo, Ɗan Bindiga, Ado Aliero Ya Jagoranci Zaman Sulhu

Ana cikin Nemansa Ruwa a Jallo, Ɗan Bindiga, Ado Aliero Ya Jagoranci Zaman Sulhu

  • Riƙaƙƙen ɗan bindiga, Ado Aliero ya halarci zaman sulhu a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya
  • Zaman sulhun ya gudana a karamar da ke jihar Katsina wanda ake zargin dan bindigan ya shirya duk da nemansa da ake yi ruwa a jallo
  • Ado Aliero ya yi jawabi ga manyan al’umma, inda ya bayyana matakan zaman lafiya tsakanin makiyaya Fulani da sauran mazauna yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Yayin da ake ci gaba da kakkabe yan bindiga a Arewacin Najeriya, wasu daga ciki sun yi zaman sulhu domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

An ce wasu daga cikinsu sun gudanar da zaman sulhu a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.

An ruwaito cewa Ado Aliero na zaman sulhu
Ado Aliero ya jagoranci zaman sulhu a jihar Katsina. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Rahoton Zagazola Makama ya yi zargin cewa riƙaƙƙen ‘yan bindiga, Ado Aliero ya halarta duk da ana nemansa ruwa a jallo kan zargin kai hare-haren ta'addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji ke hallaka yan bindiga a Arewa

Wannan zaman sulhu na zuwa ne yayin da sojoji ke ci gaba da fatattakar yan ta'adda musamman a Arewacin Najeriya.

A kwanakin nan, ɗan Ado Aliero ya sha da kyar inda ake zargin ya tsere cikin gonaki bayan wani farmaki da dakarun sojoji suka kai wa yan ta'adda.

An ce rundunar sojojin OPFY sun hallaka shahararren jagora na 'yan ta'adda da abokansa a wani harin kwanton bauna da suka kai a Zamfara.

Zamfara: Wadanda sojoji suka kashe a harin

Bincike ya nuna cewa an kashe Abdul Jamilu da Salisu tare da Auta a harin da aka kai na kwanton bauna wanda ya yi ajalin yan bindiga da dama a yankin.

Ɗan Ado Alieru, Sarki, ya tsere yayin da ake artabu, ana cece-kuce cewa 'yan ta'adda sun shiga damuwa kan yadda ake hallaka musu yan uwa da abokai.

Ado Aleiro ya yi zaman sulhu a Katsina
Dan bindiga, Ado Aliero ya jagoranci zaman sulhu. Hoto: Legit.
Asali: Original

Ado Aliero ya jagoranci zaman sulhu

Majiyoyi sun tattaro cewa a wajen zaman, Ado Aliero ya yi wa shugabannin al’umma jawabi tare da gabatar da hanyoyin da za a samu zaman lafiya.

Aliero da ake zargi da laifuka ya shiga zaman ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin cafke shi da neman karya hanyoyin ta’addancinsa.

Zaman sulhun na nuna yunƙurin kawo zaman lafiya tare da ci gaba da ayyukan sojoji don kawo ƙarshen rashin tsaro a jihar Katsina.

Ado Aliero ya rikice bayan hare-haren sojoji

A baya, mun ba ku labarin cewa rikakken ɗan bindiga, Ado Aliero, ya kira taron gaggawa bayan kashe ɗan uwansa, Isuhu Yellow, da yaran Dogo Gide suka yi a Zamfara.

Wata majiya ta tabbatar da cewa an gudanar da taron ne a sansanin Aliero da ke dajin Munhaye, ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara a Arewacin Najeriya.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa an ga ɗaruruwan ‘yan bindiga a babura suna tafiya zuwa Munhaye don halartar taron da Aliero ya kira don samar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.