Kano, Kaduna da Jihohin Arewa 14 da Ake Sa Ran Samun Ruwan Sama a Ranar Juma'a
- Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama da tsawa a fadin Najeriya a ranar 13 ga Yuni, tare da gargadin yiwuwar samun ambaliya
- A yankin Arewa, NiMet ta ce Kebbi, Kaduna, Bauchi, da Taraba za su fuskanci ruwa da safe, yayin da sauran jihohi za su iya samu da yamma
- Yankin Kudu, musamman Legas da Bayelsa kuwa, za su ga ruwan sama mai yawa, inda NiMet ta yi gargadin yin tafiya ana ruwan sama
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar 13 ga Yuni, 2025, tana mai hasashen saukar ruwan sama a wasu sassan kasar.
Hasashen ya nuna cewa za a samu ruwan sama mai hade da tsawa a Arewaci da Kudancin Najeriya, kuma za a iya samun matsalar zirga-zirga saboda guguwa.

Asali: Getty Images
Yankin Arewa: Za a yi ruwa hade da tsawa
Wannan hasashen ya yi daidai da ƙoƙarin NiMet na ci gaba da samar da bayanan yanayi a kan kari, waɗanda ke da mahimmanci ga sassan noma, sufuri da tsaron jama'a a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar NiMet, za a samu hadari da ruwan sama da safiyar ranar Juma'a din a jihohin Kebbi, Kaduna, Bauchi da Taraba.
Daga yammaci zuwa dare kuwa, wannan yanayin zai kara tsananta a Sokoto, Katsina, Kano, Zamfara, Adamawa da Gombe.
Saukar ruwan saman da tsawa da nasaba da canjin yanayi da ake fuskanta a watan Yuni, musamman a yankunan savanna wanda ake samun sauyin damina da bazara.
Yiwuwar ambaliya a FCT da jihohin Arewa ta Tsakiya
Hukumar NiMet ta kuma yi hasashen cewa za a iya samun ruwan sama da safiyar Juma'a a Abuja, da kuma jihohin Niger, Kwara da Nasarawa.
Daga bisani za a ci gaba da samun ruwan hadde da tsawa a Plateau da Kogi, da sauran yankunan da aka ambata da farko.
Hasashen ya nuna yiwuwar iska mai ƙarfi da kuma ambaliya, wanda ke iya janyo faduwar itatuwa da yawaitar katsewar wutar lantarki.
Ana shawartar mazauna yankin da su takaita zirga-zirga a lokacin ruwan sama, su kuma daure su killace kayan gida don gujewa asara.

Asali: Getty Images
Yankin Kudu: Za a samu ruwa mai yawa a Legas
A Kudancin Najeriya, NiMet ta ce za a iya samun ruwan sama da tsawa a safiyar ranar a Ondo, Edo, Rivers, Lagos, Akwa Ibom, Cross River, Bayelsa da Delta.
Daga yammaci zuwa dare kuwa, ana sa ran Enugu, Imo, Ebonyi, Abia, Anambra, Ogun, Oyo da Ekiti su ma za su samu ruwan sama.
Hasashen da hukumar ta fitar ya nuna cewa za a iya samun ruwan sama a jihohin Bayelsa da Lagos har zuwa kwanaki 250 a shekarar 2025.
NiMet ta shawarci mutane da su guji yankunan da ke fama da ambaliya, kuma su cire na’urorin lantarki yayin da ake tsawa don gujewa afkuwar gobara.
Tasirin ruwan sama ga noma a Arewa
A yankin Arewa na Najeriya, noma yana daga cikin manyan hanyoyin samun abinci da tattalin arziki, kuma mafi yawan manoma na dogaro da ruwan sama ne wajen shuka da girbin amfanin gona.
Saboda yawan bushewar kasa da karancin madatsar ruwa, galibin gonakin Arewa ba su da damar amfani da tsarin ban ruwa na zamani kamar yadda ake da shi a wasu sassan kasar.
Lokacin damina na daga watan Mayu zuwa Satumba shi ne ke ba wa manoma damar noma hatsi kamar su masara, gero, dawa, da shinkafa a wasu yankuna.
Idan aka samu jinkiri ko karancin ruwan sama, noma na iya fuskantar cikas, wanda hakan ke janyo fari da karancin abinci a cikin gida.
Saboda haka, hasashen NiMet kan ruwan sama yana da matukar muhimmanci ga manoma a Arewa.
Manoma kan duba irin waɗannan hasashen don yanke shawara kan lokacin da ya dace su soma noma.
Idan aka samu ruwan sama fiye da kima, zai iya haddasa ambaliya da lalata gonaki. Idan kuma ya yi kadan, yana iya haifar da fari da asarar amfanin gona.
Wannan yasa rahotannin yanayi kamar na NiMet ke da matukar amfani wajen taimaka wa manoma su tsira da noman su a Arewa.
Za a sheka ruwa na kwana 250 a Najeriya
Tun da fari, mun ruwaito cewa, NiMet ta yi hasashen cewa jihohi shida a Kudu za su fi samun ruwan sama a 2025, inda za su iya fuskantar ruwa har na tsawon kwanaki 250.
Jihohin da za su samu wannan ruwa mai yawa sun haɗa da Legas, Osun da wasu huɗu, yayin da Ogun da Oyo za su biyo bayansu.
A yankin Arewa kuwa, ana tsammanin ruwan sama zai sauka na tsawon kwanaki 150 zuwa 200, yayin da wasu jihohin za su samu ƙasa da haka.
Asali: Legit.ng