Daminar Bana: Za a Sheka Ruwan Sama na Kwanaki 250 a Legas da Wasu Jihohi 5

Daminar Bana: Za a Sheka Ruwan Sama na Kwanaki 250 a Legas da Wasu Jihohi 5

  • NiMet ta yi hasashen jihohi shida a Kudu za su fi samun ruwan sama a 2025, inda take hasashen z a su samu ruwa na kwanaki 250
  • Jihohin da za su samu wannan ruwa mai yawa sun hada da Legas, Osun da wasu hudu, yayin da su Ogun, Oyo za su biyo bayansu
  • A yankin Arewa kuwa, ana tsammanin ruwan sama zai sauka na tsawon kwanaki 150 zuwa 200, yayin da wasu za su samu kasa da haka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa akwai jihohi shida da za su fi ko ina fuskantar yawan kwanakin ruwan sama a 2025.

NiMet ta ce jihohin Legas, Delta, Bayelsa, Cross River, Rivers, da Akwa Ibom za su fuskanci ruwan sama na tsawon kwanaki 250 zuwa 290.

NiMet ta fitar da rahoton hasashen yawan ruwan da jihohin Najeriya za su samu a shekarar 2025
Ana walkiya da tsawa yayin da ruwan sama ke sauka. Hoto: Angelo F
Asali: Getty Images

Jihohin da zasu samu ruwa na sama da kwana 200

Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton hasashen yanayi na shekarar 2025 na hukumar NiMet, wanda aka fitar a ranar Litinin, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar NiMet, jihohin da za su biyo baya wajen samun ruwa mai yawa, tsakanin kwanaki 200 zuwa 250, sun haɗa da Ogun, Oyo, Ekiti, Osun, Ebonyi, Anambra, da Enugu.

A yankin tsakiya, ana tsammanin jihohi kamar Niger, Kogi, Benue, Plateau, Nasarawa, Kwara, da babban birnin tarayya za su samu ruwa na kwanaki 150 zuwa 200 na ruwa.

A jihohin Arewa, irinsu Sokoto, Katsina, Zamfara, Kano, Jigawa, Yobe, da Borno kuwa, ana hasashen ruwan sama zai sauka na tsawon kwanaki 110 zuwa 150 a cikin shekarar.

Hasashen NiMet kan daminar 2025

NiMet ta kuma yi hasashen cewa yawan ruwan sama na shekara-shekara a faɗin ƙasar zai bambanta daga milimita 405 a Arewacin ƙasar zuwa milimita 3,010 a yankunan bakin teku.

Rahoton ya bayyana cewa:

"An na hasashen yawan ruwan sama a faɗin Najeriya a shekarar 2025 zai kasance tsakanin milimita 405 a Arewa da milimita 3010 a jihohin bakin teku.
"Mai yiwuwa ne yawan ruwan sama na shekara-shekara a jihohin Borno, Yobe, Sokoto, da Katsina ya gaza milimita 685 a wannan shekarar.
"Ana kuma tsammanin ruwan sama a jihohin tsakiya (sassan Niger, Kwara, Plateau, Nasarawa, Benue, da FCT) zai kasance tsakanin milimita 970 zuwa 1500.
"An yi hasashen cewa jihohin Rivers, Bayelsa, Cross River, da Akwa Ibom za su sami ruwa tsakanin milimita 2700 zuwa 3010.

"Hasashen ya nuna cewa a shekarar 2025, yawan ruwan sama a mafi yawan sassan Najeriya zai zama ƙasa da wanda aka saba gani."
Hukumar NiMet ta ce akwai jihohin da za su samu ruwan sama na kasa da wanda aka saba samu
Keken A-daidaita-sahu tana tafiya a kan titi yayin da ake zabga ruwan sama. Hoto: Puneet Vikram Singh
Asali: Getty Images

Jihohin da ruwan sama zai yi karanci

Rahoton NiMet ya kuma ce ana tsammanin jihohi kamar Borno, Yobe, Sokoto, da Katsina za su sami ƙasa da milimita 685 na ruwan sama,

Yayin da jihohin tsakiya, waɗanda suka haɗa da sassan Niger, Kwara, Plateau, Nasarawa, Benue, da kuma FCT za su iya samun ruwan sama tsakanin milimita 970 zuwa 1,500.

Ana hasashen jihohin bakin teku kamar Rivers, Bayelsa, Cross River, da Akwa Ibom za su sami ruwa na tsakanin milimita 2,700 zuwa 3,010 na ruwan sama.

Za a sha ruwa da tsawa a Kaduna da wasu jihohi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, NiMet ta yi hasashen za a sami ruwa mai tsawa da iska mai ƙarfi daga ranar Lahadi zuwa Talata a Taraba, Ekiti, da wasu jihohin Najeriya.

Ana kuma sa ran za a sami ruwan sama mai tsawa a jihohin Filato, Abuja, Nasarawa, Kwara, Niger, Kogi, da kuma sassan Kudu maso Yamma.

Hukumar ta ba da shawara ga jama'a da su yawaita shan ruwa, su guji fita waje lokacin da ake tsawa, kuma su ɗauki matakan kiyaye lafiyarsu a waɗannan kwanaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.