Matasa 400,000 Za Su More a Mulkin Tinubu, an Faɗi Yadda Tsarin Tallafin Yake

Matasa 400,000 Za Su More a Mulkin Tinubu, an Faɗi Yadda Tsarin Tallafin Yake

  • Shugaban kasa ya sanar da shirin bashi na musamman ga matasa, wanda zai fara a watan Yuli, domin tallafa wa matasa 400,000 da ’yan NYSC
  • A cewar Tinubu, sama da mutum 100,000 sun riga sun ci gajiyar 'CREDICORP', ciki har da ma’aikata 35,000
  • Tinubu ya ce za a aiwatar da shirin ne ta hannun Hukumar CREDICORP, wacce ta bai wa sama da mutane 100,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnati za ta kaddamar da sabon tsarin bashi ga matasan Najeriya.

Tallafin zai taimakawa matasa wanda za a fara shirin a watan Yulin 2025 domin tallafa wa matasa 400,000.

Tinubu zai tallafawa matasa a Najeriya
Matasa 400,000 za su samu bashi daga gwamnatin Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Gwamnatin Bola Tinubu za ta tallafawa matasa

Tinubu ya yi wannan jawabi ne yayin da yake magana da zaman hadin gwiwa na majalisar dokoki don bikin ranar dimokuradiyya, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya ce za a aiwatar da shirin ne ta hannun Hukumar CREDICORP, wacce ta bai wa sama da mutane 100,000 damar samun lamuni.

Ya ce:

“Cikin kasa da shekara guda, sama da mutane 100,000 ciki har da ma’aikata 35,000 sun amfana da lamunin siyan kaya daga CREDICORP.
“Za mu kaddamar da sabon shiri a Yuli domin tallafa wa matasa 400,000 da ’yan NYSC da lamunin siyan kayayyakin rayuwa.
“Mun kuduri aniyar bai wa matasa damar samun aiki da horo ta hanyar samar da ayyuka da bunkasa kwarewa.”
Gwamnatin Tinubu za ta tallafawa matasa
Gwamnatin Tinubu ta shirya gwangwaje matasa 400,000 da tallafi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yadda Tinubu ke gyara fannin tattalin arziki

Tinubu ya ce gwamnati ta fara gyara tattalin arzikin da ya tabarbare ta hanyar daukar sababbin matakai domin magance matsalolin da ke hana ci gaba.

Ya ce gyare-gyaren sun fara yin tasiri, inda ya ce alamun ci gaban tattalin arziki sun fara bayyana a kasa, The Nation ta ruwaito.

“Muna gani, GDP ta karu da kashi 3.4 cikin dari a 2024, yayin da kashi na hudu ya kai 4.6 cikin dari, mafi girma cikin shekara 10.

“Farashin abinci na raguwa a hankali, kuma darajar Naira ta fara daidaituwa yayin da adadin kudin ajiyar kasa ya ninka sau biyar.
“Matsayin kudin shigar kasa yana da kyau yanzu, kuma kimar bashi ta kasa tana gyaruwa yayin da muke tallata kayayyakin fitarwa."

- Cewar Tinubu

Tinubu ya kuma ce gwamnati ta fara shimfida igiyoyin na’ura a fadin kasar domin bunkasa intanet da rage gibin fasaha.

Ya ce wannan shiri zai kara saurin intanet, inganta kasuwanci, taimaka wa dalibai da kuma hada al’umma ta kafar zamani.

Wani matashi ya tattauna da Legit Hausa

Kwamred Aliyu Abubakar ya ce tabbas matasa suna bukatar taimako musamman a wannan lokaci.

"Babbar matsalar da matasa ke ciki yanzu shi ne rashin aikin yi da kuma lalacewar tarbiyya.
"Muna bukatar irin wadannan shirye-shirye da za su kawo sauyi sai dai matsalar rashin isa ga hannun matasan na kawo cikas."

- Cewar Kwamred

Tinubu zai tallafawa rayuwar matasa

Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniya da 'Investonaire Academy' domin horas da matasa 100,000 duk shekara.

Ministan matasa, Ayodele Olawande ya ce matakin zai koya wa matasa dabarun kasuwanci na zamani, da horo kan ilimin kuɗi da dabarbaru.

Dr. Enefola Odiba na 'Investonaire Academy' ya ce shirin zai ƙarfafa matasa wajen yin tasiri a tattalin arziki ta hanyar samun ilimi da ƙwarewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.