Ranar Dimokuradiyya: Jami'ai Sun Kafa, Sun Tsare Yayin da ake Zanga Zanga

Ranar Dimokuradiyya: Jami'ai Sun Kafa, Sun Tsare Yayin da ake Zanga Zanga

  • Hukumomin tsaro sun baza jami’an tsaro a manyan wurare kamar yayin zanga-zangar lumana dake gudana a wasu sassan Najeriya
  • Kungiyoyi sun fara zanga-zanga a yankin Apo dake babban birnin tarayya, suna rera wakokin ƙorafi kan tsadar rayuwa da rashin tsaro
  • Jami’an tsaro na ci gaba da sanya ido domin tabbatar da zaman lafiya a Abuja yayin da yan Najeriya ke ci gaba da nuna takaicinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja’Yan sanda da jami'an DSS sun mamaye manyan tituna domin dakile tarzoma da ka iya tasowa a yayin zanga-zangar rashin tsaro da tsadar rayuwa da aka gudanar.

An tura jami’an tsaro da dama zuwa muhimman wurare a babban birnin tarayya Abuja, yayin da wasu kungiyoyi suka fara zanga-zanga.

An yi zanga-zanga
Matasa sun yi zanga-zanga a ranar dimokuradiyya Hoto: @Kolaqhazim
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta wallafa cewa matasan sun gudanar da zanga-zanga a ranar dimokuraɗiyya, domin nuna rashin jin daɗin su kan hauhawar farashi da ƙaruwar rashin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ranar dimokuradiyya: An gudanar da zanga-zanga

Punch ta ruwaito cewa an hango jami’an tsaro daga ’yan sanda, DSS da NSCDC a manyan hanyoyi da mahadar titi a fadin birnin, musamman Eagle Square.

A wuraren da aka hangi jami'an tsaro sun ba muhimmanci ga harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda ake tsammanin masu zanga-zanga za su taru.

Zanga-zangar ta soma ne a yankin Apo na Abuja, inda masu zanga-zangar suka fara gudanar da tattaki, suna rera wakokin hadin kai.

Matasa sun fusata a ranar dimokuraɗiyya
Matasa sun nemi canji a ranar dimokuraɗiyya Hoto: @Kolaqhazim
Asali: Twitter

Zanga-zanga: Jami’an tsaro na sa ido

An hango jami’an tsaron na bibiyar duk inda zanga-zangar ke gudana, suna kula da tsaron lafiyar jama’a da kare dukiyoyi domin kauce wa hargitsi ko tashin hankali.

Har zuwa yanzu dai, zanga-zangar ta kasance cikin lumana, yayin da ake ci gaba da lura da lamarin daga bangaren hukumomin tsaro.

Ana gudanar da zanga-zanga a ranar dimokuraɗiyyar da fatan nuna wa gwamnatin halin da kasa ke ciki duk da mulkin dimokuraɗiyya.

Matasan Kano sun goyi bayan zanga-zanga

Duk da matasa a Kano ba su gudanar da zanga-zanga ba, amma sun bayyana cewa sun goyi bayan fitar da aka yi a wasu jihohi.

Umar Ibrahim, guda daga cikin shugabannin kungiyoyin matasa a Kano ya ce ba su zanga-zangar lumana ba ne saboda tsaro.

Ya ce:

"Ita wannan zanga-zangar an shirya ta ne a duk Najeriya akwai jihohi da muka ga ta gudana sosai kamar irinsu Adamawa da suka yi wanda daya daga cikin bukatarsu shi ne a kawar da tsadar rayuwa."
"An bukaci gwamnati ta janye tuhume-tuhume da take wa yan Najeriya su 10 wadanda suka shiga zanga-zangar tsadar rayuwa wacce aka yi a watan Augustan shekarar da ta wuce."
"Sai dai a Kano abin bai yi tasiri ba saboda yanayin tsaro da kuma kaucewa abinda zai kawo rashin tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar."

Ya kara da shawartar yan Najeriya, musamman matasa, da su zauna a cikin shirin canja yan siyasar da ba su cancanta ba.

A cewar Umar Ibrahim:

"Muna bukatar al'umma kasar nan kowa yasan halin da ake ciki, a don haka 2027 ta zama dama ce ta sauya duk wanda bai cancanta ba, domin ganin an kwaci kai daga wannan halin."

Tinubu: "Za mu kare dimokuraɗiyya"

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ba zai karya dimokuraɗiyya ta hanyar mayar da Najeriya ƙasa mai tafiya karkashin jam’iyya ɗaya ba.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin ranar Dimokuraɗiyya da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Ƙasa, a ranar 12 ga watan Yuni, 2025.

Shugaban ƙasa ya ce Najeriya kasa ce mai yawan al’umma da ra’ayoyi daban-daban, don haka tafarkin jam’iyya ɗaya ba zai yi wa dimokuraɗiyya daidai ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.