Yadda wata 'yar aiki mai shekaru 11 ta kashe 'dan masu gida babu gaira babu dalili

Yadda wata 'yar aiki mai shekaru 11 ta kashe 'dan masu gida babu gaira babu dalili

- Mai aiki ‘yar shekara 11 a jihar Legas, ta dabawa yaron da take kula dashi wuka har lahira, dan shekara 5

- 'Yar aikin, Ojiugo Ifechukwu Duru da gangan ta hallaka yaron, bada jimawa ba bayan mahaifiyar yaron ta tafi ta barta dashi da kanensa a gidan

-Bada jimawa ba bayan fitarta gidan aka kirata data dawo gida cikin gaggawa, inda ta tarar mai aikinta ta kashe danta na fari

Wata mai aikin gida ‘yar shekara 11 a jihar Legas, ta dabawa yaron da take kula dashi waka har lahira, dan shekara 5, a unguwar Okoloko, Abule-Ado Shoba, jihar Legas.

Ojiugo Ifechukwu Duru da gangan ta hallaka yaron, bada jimawa ba bayan mahaifiyar yaron ta tafi shagonta dake kusa da gidan ta barta dashi da kaninsa a gidan.

'Yar aiki mai shekaru 11 da dabawa dan masu gida wuka, ta kashe shi har lahira
'Yar aiki mai shekaru 11 da dabawa dan masu gida wuka, ta kashe shi har lahira

Bada jimawa ba bayan fitarta gidan aka kirata data dawo gida cikin gaggawa, inda tana zuwa ta tarar da mai aikin ta ta kashe mata danta na fari, lamarin ya faru ne a ranar Asabar 10 ga watan Maris, shekara ta 2018.

Kafar yadda labarai na Yaba Left ta bayyana cewa Ojiugo ta bugi Chikamso, sannan tayi kokari shakareshi da sarka a wuyansa amma ya tsira daga wannan. Daga nan tayi amfani da wani karfe mai tsini ta daba masa a gabansa wanda hakan ne yayi sanadiyyar mutuwarsa.

KU KARANTA: Kisan da Makiyaya ke yi zai iya haddasa yaki - Gwamna Umahi

Daga nan ta juya kan kaninsa ta fara dukansa shima. Yaron dan kimanin shekaru 2 zuwa 3, ya ruga ya bar gidan zuwa makwabta. Majiya taji cewa yaron baya iya bude kofar gidan da kansa, amma a ranar azaba ta sanya ya bude.

Da isarsa makwabta ya rike matar, ta kasa lallamarsa. Inda mai aikin ta biyoshi gidan tana kokarin jansa don su koma gida, amma yaki yarda ya saki matar yana kuka wanda hakan yasa ta zargi akwai wani abu, don yaron bai taba nuna nuna irin wannan halayan ba.

‘’Ta kashe Bobo’’, abinda yaron yayi ta fada wa makwabciyar kenan. Hakan ya sa ta daukesu zuwa gidan domin ta san abunda ke faruwa, tana shiga gidan ta tarar da gawar yaron a kasa, ta daga hannunsa da kafafu amma kowane ta saki sai ya fadi kasa.

Hakan yasa ta tabbatar cewa yaron ya mutu. Sai ta kira uwar yaran da hukumar ‘yan Sanda kuma a halin yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164