Tirkashi: Za a Dauke Wutar Lantarki na Tsawon Kwana 4 a Bauchi da Jihohin Arewa 5
- Kamfanin TCN ya sanar da ɗauke wutar lantarki na kwanaki huɗu a jihohi shida na Arewa maso Gabas domin kafa sababbin turakun wuta
- Yayin aikin, tashoshin Gombe da Biu za su karɓi wuta daga Dadin-Kowa da Maiduguri, amma Yola da Jalingo za su rasa wuta gaba ɗaya
- Kamfanonin YEDC da JED sun tabbatar da cewa za a dauke wuta a wasu yankunan Adamawa, Borno, Taraba, Yobe, Gombe da Bauchi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da dauke wutar lantarki na tsawon kwanaki hudu a jere a jihohin Arewa maso Gabas.
Kamfanin TCN ya aika sako ga kamfanonin rarraba wuta (DisCos), inda ya sanar da su cewa za a dauke wuta a jihohi shida na shiyyar.

Asali: Getty Images
A cikin sanarwar da jami'in hulda da jama'a na TCN ya fitar, kuma aka wallafa a shafin hukumar na X, an ce za a dauke wutar ne domin kafa sababbin turakun wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a dauke wuta a jihohin Arewa maso Gabas
Sanarwar da ta ce za a kafa turakun wutar lantarki masu karfin 330kV a kan layukan wuta na Bauchi mai karfin 330kV.
Kamfanin TCN ya ce jihohin shida za su fuskanci daukewar wutar ne daga ranar 10 ga watan Yuni zuwa 14 ga Yuni, kuma zai shafi layin da ya kai wuta daga Bauchi zuwa Gombe.
Sanarwar ta ce:
"TCN ya fara kafa turakun wuta na turn-in-turn-out a kan layin da ke samar da wuta mai karfin 330kV wanda ya taso daga Jos-Bauchi-Gombe, don ganin an hada sabon layin wutar Bauchi mai karfin 330kV.
"Yayin da ake kafa sababbin turakun wutar, kananun tasoshin wuta na Gombe da Biu za su karbi wuta daga babbar tashar wuta ta Dadin0Kowa da ta Maiduguri tare da tallafin tashar MEPP."
Jihohi da yankunan da za a dauke wuta
Sakamakon wannan aikin, kamfanin TCN ya ce za a samu daukewar wuta ko kuma karancinta ga kamfanonin da ke rarraba wuta a Jos da Yola.
Sanarwar TCN ta kara da cewa:
"Kuma hakan zai shafi wutar da kamfanonin ke rarrabawa Bauchi, Gombe, Ashaka, Savannah, Damaturu/Potiskum da Biu.
"Yola da Jalingo ne kawai za su fuskanci daukewar wuta gaba daya a tsawon kwanaki biyar da za a shafe ana kafa sababbin turakun wutar."
Sanarwar ta kuma ce akwai sabon turken wuta da ake kan kafawa domin ganin cewa tashoshin Bauchi da Gombe suna taimakawa sauran yankuna a duk lokacin da za a yi gyara.
Kamfanin ya kuma ce idan aka kafa sabon turken, to Jos zai iya samar da wuta ga karamar tashar wuta ta Bauchi kai tsaye daga layin wuta mai karfin 132kV, idan layin 330kV da ya tafi Gombe ba ya iya aiki.

Asali: Getty Images
Kamfanonin DisCos sun magantu
Da yake tabbatar da lamarin, kamfanin rarraba wuta na Yola (YEDC) ya ce za a dauke wuta a Adamawa, Borno, Taraba da Yobe daga karfe 10:00 na safiyar Talata zuwa karfe 5:00 na yammacin Asabar, 14 ga Yuni, 2025.
Jaridar Daily Trust ta rahoto kamfanin ya ce a tsawon wadannan kwanaki, kananun tashoshin wuta na Damaturu, Molai, Yola da Jalingo ba za su yi aiki ba.
Shi ma kamfanin wuta na Jos (JED), a sanarwar da ya fitar ya ce wannan aikin da TCN zai yi zai shafi abokan huldarsa na jihohin Gombe da Bauchi.
Karanta sanarwar TCN a nan kasa:
Yadda rashin wutar zai shafi mutane
Muntari Aliyu, Yelwan Kagadama, jiha Bauchi, ya shaida wa Legit.ng cewa kwana kusan biyu kenan ba su da wuta, bai ma san cewa gyara ake yi ba har sai da wakilinmu ya tuntube shi.
A cewar Muntari, wanda ke sana'ar nika:
"Sai yanzu na san cewa gyara ake yi, mu dai mun ga kwana biyu ba a maido da wuta ba. To ka san idan damina ta yi, ana yawan samun lalacewar wutar.
"Maganar gaskiya, rashin wutar nan ba karamin kassara ni ya yi ba. Duka injina na na wuta ne, kwana biyun nan ban nika ko tiyar masara ba.
"Ba kuma zan iya tayar da janareto ba, don ba ni da shi. To gaskiya, rashin aiki na ya jefa ni da iyalaina cikin garari, domin dama sai na yi aikin ne nake samu na yi awo, na yi cefane."
Da muka tuntubi wata Rahinatu Garba Musa da ke Fadamar Mada, ta ce tana ji tana gani kunun ayar da ta yi na sayarwa ya lalace, saboda rashin wuta.
"Gaskiya an cutar da mu. Wallahi jiya na kulla kunun ayar nan da yamma, na tunanin wai za a maido wuta da daddare kamar yadda suka saba, haka muka ji shiru har safe.
"Kai abu wasa wasa har yamma, karshe na fito da shi daga firij, lokacin har ya fara bugawa. In takaita maka, haka na yi asarar kunun nan, don ba kowa ne zai iya shansa a lokacin ba."
- Rahinatu Garba Musa.
Lalacewar tushen wutar lantarki a 2025
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tushen wutar lantarki na kasa ya fuskanci matsala, lamarin da ya haddasa daukewar wuta a Najeriya, musamman jihar Legas.
Yayin da gwamnatin tarayya ke murnar cewa karfin wutar lantarki ya kai 6,000MW, rahotanni sun nuna cewa samar da wutar ya ragu zuwa kasa da 1,000MW.
A zantawar Legit Hausa da wani matashi, Gaddafi Musa, ya ba 'yan Najeriya shawarar komawa amfani da 'solar' domin samun wutar lantarki daga hasken rana.
Asali: Legit.ng