Shugaba Tinubu Ya Yi Muhimman Kalamai kan Wike, Ya ba Ministan Shawara

Shugaba Tinubu Ya Yi Muhimman Kalamai kan Wike, Ya ba Ministan Shawara

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya koma mai ba da shawara ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike
  • Mai girma Bola Tinubu ya buƙaci Wike da ya toshe kunnuwansa daga sauraron kalaman masu suka kan ayyukan da yake yi
  • Tinubu wanda ya jawo Wike cikin gwamnatinsa, ya yaba masa kan yadda yake gudanar da ayyukan ci gaba a birnin tarayya Abuja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, shawara.

Tinubu ya buƙaci Nyesom Wike, da kada ya bari masu yawan magana da masu suka su ɗauke masa hankali, kan aikinsa na sauya fasalin babban birnin ƙasar nan.

Tinubu ya yabawa Nyesom Wike
Shugaba Tinubu ya yabi Nyesom Wike Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata, lokacin da ya ƙaddamar da cibiyar taro ta ƙasa da ƙasa da aka gyara tare da sabuntawa a Abuja, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasan ya ce gyaran da aka yi wa cibiyar taron wata alama ce ta irin ƙoƙarin gwamnatinsa na sauya yadda abubuwa ke gudana a ƙasar nan.

Wace shawara Bola Tinubu ya ba Wike?

“Ina farin ciki, Nyesom Wike, kana nuna hakan. Kada ka saurari masu yawan magana da ƴan gutsiri tsoma kan duk abin da suke fada. Ci gaba da aikinka mai kyau."
"Kai shugaba ne mai sauya al’amura. Kana da hangen nesa, basira da jajircewa domin samun nasara."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatinsa na da cikakken sanin cewa samar da ababen more rayuwa na zamani, su ne ginshiƙin ɗorewar tattalin arziƙi, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

"Ta hanyar manufar ‘Renewed Hope’, mun ƙudiri aniyar sabunta kayan more rayuwa da sauran muhimman sassa kamar su sufuri, lafiya, ilimi, makamashi da cigaban birane."
“Saboda mun fahimci cewa ingantaccen kayan more rayuwa shi ne ginshiƙin tattalin arziƙi mai bunƙasa a cikin al’umma mai ci gaba da haɗin kai."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da cibiyar ICC
Shugaba Tinubu ya bukaci Wike ya maida hankali kan aikin da yake yi Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Shugaba Tinubu ya yabawa Wike

Tinubu ya ce gyaran cibiyar taron wata shaida ce ta yadda Najeriya ke da niyya wajen bunƙasa diflomasiyyar yanki, tattaunawar ciniki tsakanin ƙasashe, hadin gwiwa da ƙasashen duniya, da wasu tsare-tsare masu ma’ana.

A ƙarshe, Shugaban Najeriyan ya shaida wa abokansa na siyasa, masu riƙe da muƙaman gwamnati da ma’aikata cewa ba za a bari su riƙa amfani da cibiyar taron kyauta ba don abubuwan jin dadi ko na kamfanoni.

“Dole ne ku girmama abin da mai kula da wajen ya faɗa. Idan kuna son amfani da wannan wuri, dole ne ku biya kuɗi."

- Shugaba Bola Tinubu

Nyesom Wike a matsayin minista

Tun bayan karɓar mukamin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja a cikin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Wike ya kasance cikin jerin 'yan siyasa da suka fi jawo abin surutu a Najeriya.

Wike, wanda tsohon gwamnan jihar Ribas ne daga jam’iyyar adawa ta PDP, ya karɓi mukami daga gwamnatin jam’iyyar APC — lamarin da ya janyo muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan siyasa da al’umma.

Wasu na kallon hakan a matsayin cin amanar jam’iyyar da ya fito, musamman ganin irin rawar da ya taka a zaben 2023.

Har ila yau, salon mulkinsa a matsayin minista ya janyo masa martani daga masu sukar sa.

Wike ya fi karkata wajen amfani da karfi da saurin zartar da matakai — yana yanke hukunci cikin gaggawa, tare da fitar da umarni da wasu ke ganin suna da saukin kai ga cin zarafin dimokuraɗiyya da ka’idojin gudanar da aiki a matakin tarayya.

Baya ga haka, rikicinsa da wasu shugabannin PDP da kuma rikicin cikin gida a jihar Ribas sun kara fito da shi a matsayin jigo mai rikitarwa a sabuwar gwamnatin Tinubu.

Duk da yabawa da ayyukansa daga bangaren shugaban kasa, Wike na ci gaba da fuskantar suka daga 'yan kasa da ke ganin yana barazana ga daidaiton siyasa da ci gaban dimokuraɗiyya.

Rotimi Amaechi ya caccaki Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Chibuike Amaechi, ya yi martani mai zafi kan kalaman da Nyesom Wike ya yi a kansa.

Amaechi ya bayyana cewa bai da lokacin da zai tsaya yana ɓatawa wajen yin cacar baki da ƙananan yara.

Tsohon ministan ya nuna cewa yana sama da Wike domin shi ne wanda ya ɗauke shi aiki a lokacin da yake gwamnan Rivers.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng