Najeriya Ta Sake Fadawa cikin Duhu, Tushen Wutar Lantarki Ya Samu Matsala

Najeriya Ta Sake Fadawa cikin Duhu, Tushen Wutar Lantarki Ya Samu Matsala

  • Tashar wutar lantarki ta kasa ta fuskanci matsala, lamarin da ya haddasa katsewar wuta a wasu sassan Najeriya, musamman jihar Legas
  • Gwamnati tana murnar kai wutar lantarki zuwa 6,000MW, amma rahotanni sun nuna cewa samar da wutar ya ragu zuwa kasa da 1,000MW
  • A zantawarmu da wani matashi, Gaddafi Musa, ya ba 'yan Najeriya shawarar komawa amfani da 'solar' domin samun wutar lantarki daga hasken rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa wasu sassan Najeriya sun sake fadawa cikin duhu yayin da tushen wutar lantarki na kasar ta samu matsala.

Tashar wutar lantarki ta kasa ta fuskanci matsala a ranar Juma’a, wanda ya haddasa katsewar wuta a wasu sassan kasar musamman ma jihar Legas.

Kamfanonin rarraba wutar lantarki sun tabbatar da lalacewar tushen wutar kasar nan
Tushen wutar lantarki ta samu matsala, kamfanonin rarraba wutar sun magantu. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tushen wutar lantarki ya samu matsala

Kara karanta wannan

2027: Ministan Tinubu ya nuna sha'awar tsayawa takarar gwamna

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ke murnar karuwar wutar lantarki zuwa 6,000MW, wanda aka bayyana a matsayin babban ci gaba, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, a sabon rahoton da aka samu, an nuna cewa samar da wutar lantarkin ya ragu daga 4,000MW zuwa kasa da 1,000MW da karfe 2:00 na ranar Juma'a.

Ya zuwa karfe 5:00 na asubahin ranar, Juma’a, matsakaicin adadin wutar lantarki da aka samar ya kai 5,284MW, kafin faduwarsa zuwa 1,000MW da karfe 2:00 na rana.

Kamfanin DisCo na Ekeja ya magantu

Duk da haka, zuwa karfe 4:00 na yammacin ranar, samar da wutar ya ragu zuwa 803MW, yayin da injinan wasu tashoshin samar da wuta suka kasa komawa aiki.

Har yanzu, kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) bai yi karin haske kan lamarin ba, kuma mai magana da yawun kamfanin, Ndidi Mbah, ba ta amsa kiran waya ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun lakadawa ma'aikatan lantarki duka bayan yanke wuta a bariki

A cikin wata sanarwa, kamfanin rarraba wutar lantarki na Ikeja ya ce:

"Mun fuskanci matsalar rarraba wuta a ranar 07/03/2025 da misalin karfe 2:00."

Kamfanin ya ce yana aiki tare da hukumomi domin maido da wutar lantarki cikin gaggawa, a yankunan da yake kula da rarraba wutarsu.

Kamfanin Eko ya ce an fara dawo da wuta

Kamfanonin rarraba wuta sun magantu da tushen wuta ya samu matsala
Kamfanonin rarraba wuta sun ce an samu raguwar karfin wutar lanttarki a Najeriya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A wani ci gaba, jaridar Punch ta ce kamfanin rarraba wutar na Eko ya tabbatar da faruwar matsalar, yana mai cewa yana kokarin magance ta da wuri.

Sanarwar Eko DisCo ta ce:

"Muna aiki tare da hukumomi don dawo da wutar lantarkin. Za mu ci gaba da sabunta bayanai ga abokan huldarmu."

Daga bisani, kamfanin Eko ya tabbatar da cewa an fara dawo da wuta a wasu sassan da matsalar ta shafa.

Sanarwar ta ce:

"Muna farin cikin sanar da ku cewa an gyara matsalar da tashar wutar lantarki ta kasa ta samu, kuma an fara mayar da wuta a wasu yankuna."

Kara karanta wannan

'Dan bindiga ya tono sirrin 'yan ta'adda ga sojoji kafin 'yan uwasa su harbe shi

Kamfanin ya gode wa abokan huldarsa bisa hakurin da suka yi yayin da aka fuskanci wannan matsala.

An ba 'yan Najeriya mafita kan matsalar wuta

A zantawarmu da wani matashi, Gaddafi Musa, ya ba 'yan Najeriya shawarar komawa amfani da makamashin 'solar' domin samun wutar lantarki daga hasken rana.

Gaddafi, wanda dan jihar Kaduna ne ya ce idan mutum ya koma amfani da wuta daga hasken rana zi huta da takaicin durkushewar tushen wuta ko daukewar wutar gaba daya.

A cewar matashin:

"Yanzu kusan duk sati sai na je na sanya wa akalla gidaje uku zuwa biyar naurar inverter (mai mayar da hasken rana zuwa wutar lantarki), sabanin a shekarun baya da sai in yi wata ban fita aiki ba.
"Mutane sun gano amfanin hakan yanzu, domin ba ruwanka da an dauke wutar nepa ko ta lalace, za ka samu wutarka awa 24 ma damar ka sanya batira sama da biyu."

Kara karanta wannan

An kafa tarihi: TCN ya taka sabon matsayi na samar da wutar lantarki a 2025

Gaddafi ya shawarci 'yan Najeriya da su tara 'yan kudadensu, su hakura da janareta ko wutar lantarki su mallaki nau'rar wuta mai amfani da hasken rana.

Sojoji sun lakadawa ma'aikatan wuta duka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu sojoji dauke da makamai sun mamaye ofishin kamfanin rarraba wuta na Ikeja, da ke kusa da MITV a Legas.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru da misalin karfe 7:40 na safiyar Alhamis, inda aka ga sojojin na cin zarafin ma’aikatan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.