Gobarar Wutar Lantarki Ta Kashe Mutane Suna Barci a Jihar Gombe

Gobarar Wutar Lantarki Ta Kashe Mutane Suna Barci a Jihar Gombe

  • Hatsarin wutar lantarki ya yi sanadin mutuwar mutane biyar a Tudun-Wadan Pantami da ke jihar Gombe
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa dawo da wutar lantarki da karfi a transfoma ne ya haddasa lamarin
  • Rundunar ‘yan sanda ta ce an fara bincike domin gano musabbabin tashin wutar da kuma daukar matakin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Gombe ta tabbatar da aukuwar gobara saboda wutar lantarki da safiyar Asabar, 14 ga Yuni, 2025 a unguwar Tudun-Wadan Pantami.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne sakamakon zuwan wuta da karfi a transfoma da ke kusa da yankin.

Gobara ta kashe mutane a Gombe
Mutane 5 sun mutu a sanadiyyar gobara a Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli|Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda hadarin ya faru ne a cikin wani sako da DSP Buhari Abdullahi ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ta ce mutane biyar sun rasa rayukansu a sakamakon lamarin, yayin da wasu 13 ke jinya a asibitoci daban-daban da ke jihar Gombe.

An kwashe gawarwaki zuwa asibitocin Gombe

Bayanan farko daga binciken da aka gudanar sun nuna cewa hatsarin ya auku da misalin ƙarfe 1:00 na dare, inda wuta ta afka wa layukan wutar lantarki har ta shafi gidajen da ke kusa.

An bayyana cewa daga cikin gawarwakin da aka kwashe:

(i) Ai kai gawarwaki uku dakin ajiyar gawa na Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) Gombe.

(ii) An kai guda ɗaya Asibitin Gwamnati na jihar Gombe.

(iii) Sauran guda ɗaya kuwa an ajiye ta a dakin ajiyar gawa na Bolari Filin Kwallo.

‘Yan sanda daga caji ofis na Low-cost sun kai dauki a yankin domin hana karuwar hadura da kuma kwashe waɗanda suka jikkata zuwa cibiyoyin lafiya mafi kusa.

Rundunar ‘yan sanda ta nuna alhini

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gombe, CP Bello Yahaya ya bayyana matukar alhini kan aukuwar lamarin tare da jajanta wa iyalan mamatan.

Ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata yana mai cewa rundunar za ta gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin hatsarin da daukar matakin da ya dace.

Yan sanda na bincike kan gobarar Gombe
Yan sanda na bincike kan gobarar Gombe. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Rundunar ta bukaci jama'a da su kwantar da hankalinsu tare da bayar da hadin kai ga hukumomi domin hana faruwar irin wannan mummunan lamari a gaba.

Ana sa ran jama'a za su samu cikakken bayani a kan abin da ya faru da zarar rundunar 'yan sanda ta kammala bincike.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa a Benue

A wani rahoton, kun ji cewa an kama wani matashi a jihar Benue bisa zargin kashe mahaifiyarsa bayan ya mata dukan kawo wuka.

Rahotanni da Legit ta samu sun tabbatar da cewa an garzawa da mahaifiyar matashin asibiti amma likita ya tabbatar da mutuwar ta a lokacin da ake kokarin ceto ta.

Makusantan matar sun bayyana cewa an samu sabani ne a tsakanin mahaifiyar da danta wanda har ya kai ga mata jina jina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng