Kolmani: Gwamnatin Gombe, Bauchi Sun Gana da Wakilan NNPCL domin Neman Mafita

Kolmani: Gwamnatin Gombe, Bauchi Sun Gana da Wakilan NNPCL domin Neman Mafita

  • Jami’an gwamnati daga Gombe da Bauchi sun gana da wakilan kamfanin NNPCL domin warware matsalolin aiki a filin rijiyar Kolmani
  • Kwamitin hadin gwiwa ya gano matsaloli hudu ciki har da rashin biyan wasu kudi da matsalar sadarwa tsakanin kamfanoni da al’umma
  • Sun cimma matsaya akan biya kudin filaye, gudanar da binciken, da kafa tsari na sadarwa tsakanin masu ruwa da tsaki da kamfanonin mai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Jami’an gwamnati daga Gombe da Bauchi sun yi wata ganawa game da hako rijiyar man Kolmani a birnin Gombe.

An gudanar da taron na kwanaki biyu da wakilan NNPCL da suka hada da NEPL da AOML da ke aikin hakar mai na Kolmani domin warware matsalolin aiki.

An yi ganawa kan man Kolmani a Gombe
Jami'an Gwamnatin Gombe, Bauchi sun gana kan man Kolmani. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Asali: Facebook

Kolmani: An gana tsakanin Gombe, Bauchi

Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma an yi taron ne domin gyara kura-kurai da aka gano da nufin kaucewa irin matsalolin da ke faruwa a wasu yankunan da ake hakar mai.

Kwamishinan makamashi na Gombe, Sanusi Ahmed Pindiga, ya bayyana cewa kwamitin hadin gwiwa ya gano manyan matsaloli guda hudu a filin man Kolmani.

Ya ce matsalolin sun hada da mallakar filaye, rashin biyan kudin damar fara aiki (FTO), sakaci daga AOML da kuma matsalar sadarwa da al’umma.

Don magance wadannan matsaloli, an yanke shawarar cewa AOML zai gabatar da takardun biyan filaye kafin a kammala tsarin mallaka.

Kazalika, NEPL zai sa ido wajen tabbatar da AOML ya biya kudin FTO domin ci gaba da hako mai a wurin.

Matakan da aka dauka a yankin Kolmani

Za a gudanar da cikakken bincike a cikin al’ummomin da abin ya shafa domin jagorantar aikin al’umma yadda ya kamata.

An ce za a kafa tsarin sadarwa mai inganci domin tabbatar da ingantaccen mu’amala tsakanin kamfanonin man da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya kara da cewa:

“Wadanda suka halarci taron sun nuna godiya kan wannan mataki kuma sun jaddada kudirinsu na ganin an ci gaba da aikin.
“Hakanan sun bayyana fatan ganin burin hakar mai a Arewa ya tabbata domin ci gaban tattalin arziki.”
An gana a Gombe kan matsalolin hakar man Kolmani
Gwamnatin Gombe ta yi zama da na Bauchi kan man Kolmani. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Asali: Facebook

Musabbabin rigima game da iyaka kan Kolmani

Babu wani jami’in Bauchi da ya amsa tambayoyi bayan taron wanda ake sa ran zai warware takaddama kan mallakar yankin tsakanin jihohin.

Tun farko, za a iya tuna cewa an gano filayen man ne tun lokacin tsohuwar jihar Bauchi kafin kirkiro Gombe a shekarar 1996, lamarin da ya janyo rikicin mallakar wurin.

Wannan rikici ya jawo matsin lamba tsakanin al’ummomin yankin, musamman ganin muhimmancin wannan wuri mai a tattalin arzikin yankin.

Tinubu ya goyi bayan hakar rijiyoyin Kolmani

A baya, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayar da lasisin aiki na dukkan matakan da ake buƙata don aiwatar da aikin haƙar mai a Kolmani.

Ministan albarkatun mai ya ce wannan matakin na da nufin ƙara yawan haƙar mai tare da amfani da dukkan damar da ake da ita.

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya gode wa gwamnatin tarayya bisa wannan aiki, yana cewa zai amfani ƙasa baki ɗaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.