Hajjin Bana: Malamai Sun yi wa Bola Tinubu Addu'a a Birnin Madina
- Tawagar Limaman NAHCON ta gudanar da addu'o'i a Madina domin roƙon zaman lafiya da ci gaban Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa addu'o'in sun haɗa da neman nasara ga shugaba Bola Tinubu wajen tafiyar da mulki
- Limaman sun yaba da yadda NAHCON ke tafiyar da aikin Hajji, inda suka ce an samu ci gaba fiye da shekarun baya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Madina - Tawagar limaman NAHCON da ke kula da shirye-shiryen Hajji ta gudanar da zaman addu’a na musamman a birnin Madina domin Najeriya da shugabanninta.
Addu’ar ta haɗa da neman taimakon Allah ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da dukkan shugabannin siyasa a ƙasar, tare da roƙon zaman lafiya da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

Asali: Facebook
Rahoton Radio Nigeria ya nuna cewa malaman sun yaba da yadda aikin hajjin bana ke tafiya karkashin NAHCON.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban tawagar Iimaman daga jihar Legas, Sheikh Afini Abdulbari ya shaida wa manema labarai cewa zaman addu’an na da nufin tallafawa ƙoƙarin Tinubu na kyautata Najeriya.
Malamai sun yi wa Tinubu addu'a a Madina
Sheikh Abdulbari ya bayyana cewa tun bayan hawansa mulki, shugaban ƙasa Tinubu ya nuna ƙwazo da jajircewa, kuma bai nuna gajiya wa ba.
Daily Nigerian ta ruwaito malamin ya ce:
“Shugaban ƙasa ya kama aiki tun daga rana ta farko, kuma har yanzu bai nuna kasala ba.
"Saboda haka, ya kamata mu ci gaba da masa addu’a domin Allah ya taya shi jagorantar Najeriya zuwa tudun mun tsira,”
Ya ƙara da cewa:
“Mun yi addu’a ga Allah ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, tare da ba wa shugabannin siyasa nasara a aikinsu.”
An yi addu’ar ne a masallacin Annabi a Madina
Limaman da NAHCON ta zaɓo daga jihohin Legas, Osun da Oyo ne suka jagoranci zaman addu’ar a Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina
Rahotanni sun nuna cewa mahajjata daga sassa daban-daban na Najeriya sun halarci zaman addu'ar.
Addu’ar ta mayar da hankali kan neman zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar, tare da roƙon Allah ya tabbatar da shugabanci nagari a Najeriya.
Limaman sun yaba da kokarin NAHCON
Sheikh Abdulbari ya yaba da ƙoƙarin hukumar NAHCON, musamman yadda ake sauke mahajjata daga Najeriya zuwa Saudiyya, wurin saukar su, da abinci a Madina.
A cewarsa:
“An samu gagarumin cigaba idan aka kwatanta da shekarun da suka gabata, NAHCON ta inganta harkokin Hajji sosai.”

Asali: Facebook
Shi ma wani malami daga cikin tawagar, Sheikh Ridwan Mustapha Sunusi, ya ce zaman addu’ar wata hanya ce ta taimakon gwamnati don gina ƙasa mai inganci.
Ya kuma ja hankalin mahajjata da su mutunta dokokin Saudiyya da bin ƙa’idojin addini da na Najeriya yayin gudanar da ibada a ƙasa mai tsarki.
Yahaya Bello ya yi wa Tinubu fatan alheri
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi wa Bola Tinubu fatan samun nasara a 2027.
Yahaya Bello ya yi wa Bola Tinubu fatan samun nasara ne yayin da yake karyata rade radin cewa zai yi takara a zabe mai zuwa.
Tsohon gwamnan ya ce Bola Tinubu ya yi ayyuka masu yawa da za su sanya shi ya samu karbuwa a zukatan 'yan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng