Hukumar NAHCON Ta Gargadi Mahajjata kan Zamansu a Saudiyya
- Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ja kunnen mahajjatan Najeriya kan zaman da za su yi a ƙasa mai tsarki watau Saudiyya
- NAHCON ta gargaɗi mahajjatan kan ɗaukar abubuwan da suka ɓace yayin da suka gudanar da ibadah a masallacin Ka'aba
- Hukumar NAHCON ta kuma buƙaci mahajjatan da su riƙa shan ruwa sosai saboda irin zafin rana da ake yi a kasar Saudiyya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta yi gargadi ga mahajjata da su guji ɗaukar abubuwan da suka ɓace a ƙasa yayin aiwatar da Tawaf (Zagaya Ka'aba).
Hukumar NAHCON ta gargaɗi mahajjatan daga ɗaukar abubuwan ne domin kaucewa a yi musu kallon ɓarayi.

Asali: Twitter
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Alhazai ta jihar Kaduna, Yunusa Makarfi, ne ya bayyana hakan a yayin taron ba da horo ga ƙungiyar yaɗa labarai ta ƙasa da aka gudanar a Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin yanzu, hukumar ta yi jigilar mahajjata 32,549, wanda ya kai kaso 79.1% na yawan waɗanda ake sa ran za su halarci aikin Hajjin shekarar 2025.
Hukumar NAHCON ta ja kunnen mahajjata
Yunusa Makarfi ya bayyana cewa haɗarin ɗaukar abin da ya ɓace yayin Tawaf shi ne, ana iya ɗaukar mutum da laifin sata koda kuwa yana da niyyar kirki.
“Wurin yana ƙarƙashin dubban kyamarori masu bibiyar kowane motsi. Za a iya nazarin bidiyo don gano wanda ya ɗauki kayan da suka ɓace, kuma ba zai tsira daga hukunci ba."
"Don haka idan ka ga wani abu a ƙasa da ba naka ba, kada ka ɗauka. Masu sata na ko’ina, za a iya ɗaukar ka a matsayin ɗaya daga cikinsu."
- Yunusa Makarfi
NAHCON ta ba mahajjata shawara
Hukumar ta kuma ja hankalin mahajjata da su tabbatar da cewa ba su zauna cikin jin ƙishirwa ba saboda zafin rana da ake sa ran za a samu a Saudiyya.
Mataimakiyar daraktan yaɗa labarai na hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta buƙaci mahajjatan da su riƙa shan ruwa a kodayaushe.
“Ba sai ka ji ƙishirwa ba kafin ka sha ruwa, a guji zafin rana ta hanyar kauce wa rana mai tsanani."
- Fatima Sanda Usara

Asali: Twitter
Ta kuma shawarci mahajjata da su rika amfani da laima, huluna, ko su kasance a inda ake inuwa domin guje wa zafin rana.
An ƙiyasta cewa mutane 64,188 daga Najeriya za su halarci aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya.
Shettima ya gargaɗi shugaban NAHCON
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya aika da saƙon gargaɗi ga shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON).
Mataimakin shugaban ƙasan ya gargaɗi Farfesa Abdullahi Saleh da ya guji gudanar da harkokin hukumar kamar don shi kaɗai aka yi ta.
Gargadin na Kashim Shettima na zuwa ne bayan an shigar da ƙorafi kan yadda shugaban na NAHCON ya saba ƙa'idoji wajen gudanar da ayyukan hukumar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng