Bayan Taso Shi a Gaba, Sarkin Daura Ya Tuɓe Rawanin Basarake kan Zargin Ta'addanci

Bayan Taso Shi a Gaba, Sarkin Daura Ya Tuɓe Rawanin Basarake kan Zargin Ta'addanci

  • Sarkin Daura, Alhaji Faruq Faruq ya dauki mataki kan dagacin kauyen Mantau, Iliya Mantau, saboda wasu zarge-zarge
  • Sarkin ya tuɓe basaraken bayan zargin da ake yi masa na garkuwa da mutane da kuma fyade ga wata mata a Yarmaulu
  • Matasa sun yi zanga-zanga bayan jinkirin da masarautar ta yi wajen daukar mataki, duk da al’amarin yana gaban kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Daura, Katsina - A kwanakin baya, matasa sun yi zanga-zanga game da zargin wani Sarki da goyon bayan yan bindiga.

An yi zanga-zangar ne domin bukatar gwamantin Katsina da masarautar Daura ta dauki mataki kan basaraken.

Sarki ya tuɓe basarake a Katsina
Sarkin Daura ya cire dagacin kan zargin ta'addanci. Hoto: Masarautar Daura.
Asali: Facebook

Sarkin Daura ya cire dagaci a Katsina

Sarkin Daura, Alhaji Faruq Faruq ya tube Iliya Mantau, dagacin kauyen Mantau da ke Yarmaulu, karamar hukumar Baure a wani bidiyo da Muhammad Aminu Kabir ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daukar matakin ya biyo bayan zargin da ake yi masa da hannu a garkuwa da mutane da kuma fyade.

Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, bayan korafin da jama’ar Yarmaulu suka shigar, wanda ya janyo zanga-zangar matasa makon da ya gabata.

Majiyoyi sun gano cewa matasan da suka yi zanga-zangar sun zargi Sarkin kauyen da aka tube, Iliya Mantau, da wasu da yin garkuwa da Zulaihatu da jaririnta.

Sannan sun yi zargin basaraken ya yi mata fyade bayan sun karɓi fansar makudan kudi har N20m, cewar rahoton Punch.

Sarkin Daura ya tuɓe dagaci daga sarauta
Sarkin Daura ya cire dagacin kauye a Katsina. Hoto: Legit.
Asali: Original

Gargadin da Sarkin Daura ya yiwa al'umma

Lamarin ya janyo cece-kuce sosai, musamman ganin cewa masarautar Daura ta jinkirta daukar mataki har kusan shekara guda, duk da cewa shari’ar tana kotu.

Yayin da yake sanar da tube shi, Sarkin Daura ya jaddada cewa masarautar Daura ba za ta lamunci cin zarafi ga talakawa ko kadan ba.

Ya kara da cewa kofar masarautar Daura a bude take ga duk wanda ke da koke ko korafi dangane da rashin adalci ko cin zarafi.

Ya ce:

“Ina so in bayyana cewa idan wani yana ganin an cuce shi, ko ɗana ne ya aikata hakan, a kawo koke, wannan masarauta ce ta talakawa.
“Wannan masarauta ta taba tube wani sarki da ta naɗa, kuma Sarki Abdurrahman ya taba saka ɗansa a kurkuku saboda laifi. Ba za mu lamunci zalunci ba."

Sarkin Daura ya kuma ja kunnen jama’a kan yada jita-jita marasa tushe, yana mai cewa su ci gaba da bin doka da bayyana koke-kokensu ta hanyar da ta dace.

Ta'addanci: An bukaci tube Sarki daga sarauta

A wani labarin wasu mazauna garin Yanmaulu a Baure da ke jihar Katsina, sun nemi a dakatar da mai rikon sarautar yankinsu, Iliya Mantau.

Matasan da suka yi zanga-zanga sun ce Mantau ya shafe wata takwas a tsare kan sace Zulaihat Sidi da jaririnta, inda mijinta ya biya fansar N20m.

Al’umma sun bukaci Gwamna Dikko Umaru Radda ya sa baki, su na gargadi cewa sakin Mantau zai dawo da matsalar tsaro a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.