Sanatoci 18 Sun Gamu da Matsala, An Hana Jirgin Saman da Ya Ɗauko Su Sauka
- Sanata David Jimkuta ya nuna ɓacin ransa kan yadda aka hana saukar sanatoci 18 da ya gayyato zuwa wurin taron rabon kayan tallafi
- Jimkuta ya ce makircin siyasa aka sanya wajen hana jirgin da ya ɗauko sanatocin sauka a filin jiragen sama na Kashimbila a jihar Taraba
- Ya ce matsalar ba za ta hana shi aiwatar da abubuwan alherin da ya yi niyya ba, yana mai cewa mutane da yawa sun koma gida da farin ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba - Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu a Majalisar Dattawa, David Jimkuta, ya koka kan hana jirgin saman da ke dauke da sanatoci 18 sauka a filin jirgin Kashimbila.
Daga cikin sanatocin da jirgin saman ya ɗauko har da shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele.

Kara karanta wannan
"Ku bi a hankali," Omokri ya bukaci CAN ta guji shari’a da jihohi kan hutun Ramadan

Asali: Facebook
An hana jirgin sanatoci sauka a Taraba
Sanatan ya ce wannan mataki na hana jirgin da suka biyo sauka a Taraba ya jawo rashin halartarsu wurin taron rabon tallafin da ya shirya a mazaɓarsa, Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Jimkuta ya bayyana hakan ne a Wukari yayin rabon kayayyakin tallafi ga mutanen Wukari, Takum, Donga, Ibbi da Ussa da ke mazaɓar kudancin Taraba.
Ya ce sanatocin da ya gayyata ba taron kaɗai za su halarta ba, har ma za su duba wasu kudirorin dokokin da ya gabatar a Majalisar Dattawa.
Dalilin gayyato sanatocin zuwa taron
"Mun bukaci izinin saukar jirgin sanatoci 18 a Kashimbila, amma an ce mana hasumiyar filin tana da matsala kuma sai mun biya Naira miliyan 30.
"Haka na lale kudin nan na biya su, amma daga bisani sai suka ɓullo da wata matsalar, suka ce mani filin ya daina aiki kuma ba za a iya amfani da shi ba sai bayan makonni biyu," in ji Jimkuta.

Kara karanta wannan
Bola Tinubu ya ware sama da Naira biliyan 700 a watan azumi, za a yi muhimman ayyuka
Sanatan Taraba ta Kudu ya ƙara da cewa an yi duk wani yunkuri na hana wannan taron na rabon kayan arziki ga jama'a, amma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba, rahoton Premium Times.
Jimkuta ya ce duk wani yunkuri da makircin da aka ƙulla don daƙile taron raba tallafin amma da ikon Allah, "A yau mutane da dama za su koma gida da murmushi."
Abin da sanatocin za su yi a Taraba
A cewarsa, da sanatocin sun samu damar zuwa, za su duba wasu daga cikin kudirorin da ya gabatar, irin su kafa Jami'ar Tarayya a Wukari, gina gadar Ibbi da gyara titin Wukari-Jalingo-Numan.
A taron, Sanata Jimkuta ya raba kayayyakin tallafi da suka hada da motoci 70, babura 150, injinan niƙa 70, da kekunan ɗinki.
Sauran kayayyakin da sanatan ya rabawa mutane sun haɗa da Keke Napep, injinan firji, kayan wanki na mota, injinan gyaran taya da kujerun guragu.
Sanatan Kwara ya raba tallafin sana'o'i
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Saliu Mustapha na jihar Kwara ya bai wa mutane fiye da 2,500 tallafi domin bunkasa harkokin kasuwanci, noma, da sana’o’in hannu.
Sanata Saliu, mai wakiltar Kwara ta Tsakiya (APC), ya raba kayan tallafi ga mata, manoma, da masu sana’o’i a birnin Ilorin na jihar Kwara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng