Iska Mai Ƙarfi Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 27 cikin Dare a Hatsarin Jirgin Ruwa
- Wani hatsarin jirgin ruwa ya halaka mutum 27 a Gbajibo, karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara, yayin dawowa daga kasuwa a jihar Niger
- Wani wanda ya tsira daga hatsarin ya ce jirgin ya kife ne saboda yawan fasinjoji da kuma iska mai karfi daga hadari
- Shugaban karamar hukumar ya ce gwamnati za ta haramta tafiya da daddare tare da wajabta amfani da jaket din ceton rai a ruwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Wani hadarin jirgin ruwa ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 27 a kauyen Gbajibo da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara.
Hatsarin jirgin ya faru ne kasa da watanni bakwai bayan wani hatsari makamancin haka ya kashe mutane 100 a yankin.

Asali: Original
Mutane sun mutu a hatsarin jirgin ruwa
An samu labarin cewa jirgin ruwa na dauke da fasinjojin da ke dawowa daga kasuwa a jihar Niger ne lokacin da ya kife, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani shaidan gani da ido kuma wanda ya tsira daga hadarin ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne daren kwana uku da suka gabata.
Ya ce:
“Jirgin ya kife ne saboda an dora masa fasinjoji fiye da kima, kuma iska mai karfi daga hadari ta taimaka.”
Duk da bai san adadin fasinjojin da ke cikin jirgin ba, ya ce iska mai karfi daga hadari na daga cikin abubuwan da suka haddasa lamarin.
Shugaban karamar hukumar Kaiama, Abdullah Danladi, ya jagoranci tawagar gwamnati domin jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.
Ya ce gwamnati ba za ta yarda da irin wannan lamari da ke faruwa kusan kowace shekara ba a yankin.
Danladi ya bayyana cewa za a kafa kwamiti da zai tabbatar da amfani da jaket din ruwa da kuma haramta tafiya da daddare.

Asali: Facebook
Sarki ya kadu da abin da ya faru
Hakazalika, Sarkin Kaiama, Alhaji Muazu Umar, ya ce za su kara wayar da kan jama’a kan matakan kiyaye hadurran ruwa.
A watan Oktoban bara, mutum kusan 60 yawanci mata da yara sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a Gbajibo, Vanguard ta ruwaito.
Jirgin da aka ce na katako ne kuma ya dace ya dauki mutum 100, amma ya na dauke da kimanin mutum 300 lokacin da ya kife.
Kwana biyu bayan hadarin, Shugaba Bola Tinubu ya yi jimami da mutuwar mutane, ya kuma jajanta wa iyalan mamatan.
Ya umurci Hukumar Kula da Ruwa ta Kasa (NIWA) da ta binciki yawaitar hadurran jiragen ruwa a Neja da sauran wurare.
Yan fashin teku sun sace mutane 10
Mun ba ku labarin cewa yan fashin teku sun tare jirgin ruwa, sun yi awon gaba da fasinjoji 13 a kogin Idaka da ke ƙaramar hukumar Okrika a jihar Rivers .
Maharan sun kuma kwace wasu jiragen ruwa biyu da suka ɗauko kayayyaki amma daga bisani an ji cewa an yi nasarar ƙwato su.
Shugaban kungiyar ma'aikatan sufurin ruwa (NWU) ya nemi Kantoma ya gaggauta ɗaukar mataki domin abin na neman wuce gona da iri.
Asali: Legit.ng