Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Ta'addan Boko Haram a Borno

Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Ta'addan Boko Haram a Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar daƙile harin da Boko Haram suka kai a jihar Borno bayan an kwashi lokaci ana ɗauki ba daɗi
  • Sojojin waɗanda suka samu taimakon jiragen yaƙi sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 16 a farmakin ɗa suka kawo a garin Damboa
  • Bayan ragargazar ƴan ta'addan, sojojin sun kuma bi sawun ragowar waɗanda suka tsere zuwa cikin daji domin ganin an cafko su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya da ke ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun samu nasara kan ƴan ta'addan ISWAP/Boko Haram a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar daƙile wani hari da ƴan ta’addan suka kai a garin Damboa da ke jihar Borno.

Sojoji sun hallaka 'yan Boko Haram a Borno
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta sanya a shafinta na X a ranar Juma'a, 23 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka yi artabu da ƴan Boko Haram

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar 23 ga watan Mayu, dakarun sun hangi ƴan ta’addan a Damboa, inda suka fara musayar wuta da su nan take.

Dakarun sun samu goyon baya daga jiragen yaƙin sojojin saman Najeriya, inda musayar wutar ta ɗauki kusan sa’o’i biyu.

Sanarwar ta ce aƙalla ƴan ta’adda 16 aka kashe a yayin musayar wutar da aka yi.

“Babban abin da ƴan ta’addan suka nufa shi ne kai hari kan sansanin rundunar, wanda hakan ya sa aka gaggauta tura sojojin sama domin tallafawa dakarun da ke ƙasa."
"Bayan kusan sa’o’i biyu ana ɗauki ba daɗi mai zafi, sojojin sun tilastawa ƴan ta’addan tserewa bayan kashe su da raunata wasu daga cikinsu."
"Dakarun sun samu nasarar kashe ƴan ta’adda 16 a fafatawar, kuma a halin yanzu suna ci gaba da gudanar da samamen bin sawu domin kama waɗanda suka tsere."

"Duk da cewa an sami nasarar murƙushe harin, ɗaya daga cikin makaman da ƴan ta’addan suka harba ya samu wani wurin ajiyar makamai, sai dai an yi gaggawar shawo kan lamarin ba tare da wata ɓarna ba."

- Rundunar sojoji

Sojoji sun ragargaji 'yan Boko Haram
Sojoji sun dakile harin 'yan ta'addan Boko Haram Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Karanta wasu labaran kan ƴan Boko Haram

Abin a yaba ne

Ibrahim Sanusi ya shaidawa Legit Hausa cewa ya yi farin ciki sosai da samun labarin nasarar da sojojin suka samu kan ƴan ta'adda.

"Irin waɗannan labaran muke fatan samu a kodayaushe na cewa sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda."
"Muna yi musu addu'ar Allah ya ci gaba da ba su kariya da nasara a yaƙin da suke yi da miyagun ƴan ta'adda."

- Ibrahim Sanusi

Zulum ya magantu kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwa kan yadda ƴan ta'adda ke cin karensu babu babbaka.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa a yanzu ƴan ta'adda sun fi amfani da makamai masu kyau fiye da dakarun da ke fafatawa a fagen daga

Zulum ya yi kira ga jihohi da gwamnatin tarayya ds su yi haɗin gwiwa domin kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng