Ana murna Kamfanin NNPCL Ya Rage Farashin Fetur, 'Yan Kasuwar Mai na Kukan Asara

Ana murna Kamfanin NNPCL Ya Rage Farashin Fetur, 'Yan Kasuwar Mai na Kukan Asara

  • Kamfanin NNPCL ya rage farashin fetur zuwa N880 a Legas da N935 a Abuja, lamarin da ya jefa ’yan kasuwa cikin babbar asara
  • Dangote da abokan hulɗarsa kamar MRS da Ardova suma sun sauke farashin fetur, abin da ya kawo sabuwar gasa a kasuwar man fetur
  • IPMAN ta ce yanzu 'yan kasuwa ne ke fuskantar babbar asara yayin da talakawa ke amfana da raguwar farashin man fetur a Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - ’Yan kasuwar mai sun nuna cewa suna tafka asara yanzu da kamfanin NNPCL ya rage farashin litar fetur zuwa N880 a wasu sassan kasar.

A ranar Litinin, muka ruwaito cewa NNPCL ya saukar da farashin litar fetur daga N925 zuwa N880 a Legas, sannan ya sauke litar daga N950 zuwa N935 a Abuja.

'Yan kasuwa sun koka da NNPCL ya rage farashin man fetur
Masu ababen hawa na dogon layi a daya daga cikin gidan man NNPCL. Hoto: Anadolu
Asali: Getty Images

NNPCL, Dangote sun rage farashin fetur

Sauke farashin na NNPCL ya biyo bayan matakin da matatar man Dangote ta dauka na rage farashinta daga N865 zuwa N835 a defo, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Dangote ta bukaci abokan hulɗarta kamar su MRS, Heyden da Ardova su sayar da litar fetur din a kan N890 maimakon N920 a Legas.

A Kudu maso Yamma kuwa, litar fetur din ta koma N900, a Kudu maso Kudu kuma N910, yayin da a Arewa maso Gabas ake sayar da litar a kan N920.

Wasu gidajen man NNPCL ba su sauya farashi ba

Rahotanni sun nuna cewa sabon farashin NNPCL ya kasance ƙasa da na Dangote da bambancin N10, abin da ke nuna cewa za a iya samun sabuwar gasa.

Wata majiya ta ce wasu gidajen man NNPCL na ci gaba da sayar da man a tsohon farashi domin su fara mayar da kudinsu na tsohon man da suke da shi.

Hammed Fashola, mataimakin shugaban IPMAN, ya tabbatar da saukar farashin, yana mai cewa ’yan kasuwa na tafka asarar kudi yanzu.

'Yan kasuwa na asara bayan rage farashin mai

Ya ce sashen da ke sayar da man NNPC ya fitar da sanarwa ga gidajen mansa da su rage farashin fetur din zuwa N880, inda wasu suka riga sun fara aiki da shi.

"An tabbatar da rage farashin man fetur zuwa N880 a Legas, yayin da wasu suke sayar da shi a kan tsohon farashinsa na N910" inji Fashola.

Ya kara da cewa sauyin farashin ya shafi ’yan kasuwa kai tsaye saboda suna asara ne kawai a yanzu yayin da suke kokarin sayar da tsohon fetur dinsu.

Hammed Fashola ya bayyana cewa kodayake saukar farashi alheri ne ga talakawa, amma ’yan kasuwa su ke shan kashin karin da aka yi.

IPMAN ta koka kan yadda sauke farashin fetur da NNPCL ya yi ke barazana ga 'yan kasuwa
Dandazon mutane ke bin layin sayen man fetur a wani gidan mai a Najeriya. Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: UGC

"Talakawa ne ke amfana da ragin" - IPMAN

Mataimakin shugaban IPMAN din ya kara da cewa:

"Ina tabbatar muku da cewa ’yan kasuwa na asarar kudi sosai. Wannan shi ne gaskiyar magana.

Ya ce talakawa za su fi amfana da sabon farashin, yayin da a hannu daya hawa da saukar farashin man na tilasta wa ’yan kasuwa su yi asara.

Fashola ya jaddada cewa:

“A bangaren talakawa, farashi ya sauka. Wannan shine ribar cire tallafi. Amma mu ’yan kasuwa, mu ke daukar radadin sauyin.

Lokacin da aka tambaye shi hanyoyin rage asara, Fashola ya ce, “dole mu sayar da tsohon kaya cikin gaggawa domin kauce wa babbar asara.”

Farashin fetur zai ci gaba da sauka a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, masanin tattalin arziki, Bismarck Rewane, ya bayyana cewa ana sa ran farashin fetur zai ci gaba da sauka har zuwa Yunin 2025.

Ya fadi haka ne bayan matakin da Dangote da NNPCL suka dauka na rage farashin, wanda zai saukaka wa 'yan Najeriya radadin tsadsar rayuwa.

A cewarsa, gogayya da ke tsakanin kamfanin Dangote da NNPCL a kasuwa za ta amfani masu amfani da fetur tare da saukaka musu farashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.