Ayyuka 11,122 da Ake Zargin 'Yan Majalisar Tarayya Sun Cusa a Kasafin Kudin 2025

Ayyuka 11,122 da Ake Zargin 'Yan Majalisar Tarayya Sun Cusa a Kasafin Kudin 2025

  • BudgIT ta zargi ‘yan majalisar tarayya da cusa ayyukan da darajarsu ta kai N6.93trn a kasafin 2025 ba tare da cikakken bayani ba
  • Rahoton ya ce an cusa ayyuka 11,122 ciki har da manyan ayyuka 238 da kowanne ya haura N5bn, wanda ko kadan ba su da amfani ga kasa
  • BudgIT ta ce wasu ma’aikatu kamar NCAM sun samu kudin ayyukan da ba su cancaci samu ba, sai dai majalisa ta musanta zarge-zargen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A cikin wani rahoto mai daukar hankali, ƙungiyar BudgIT ta zargi 'yan majalisar tarayya da cusa ayyuka da suka kai kimanin Naira tiriliyan 6.93 a cikin kasafin kuɗin 2025.

Kungiyar ta bayyana cewa 'yan majalisar sun cusa wadannan ayyuka ba tare da cikakken bayani ko daidaito da muradun ci gaban ƙasa ba.

Kungiyar BudgIT ta zargi majalisar tarayya da cusa ayyuka 11,122 da kudinsu ya kai N6.93trn a kasafin 2025
Shugabannin majalisar tarayya, Godswill Akpabio, Tajudeen Abbas tare da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

BudgIT na zargin an yi cushe a kasafin 2025

BudgIT wata ƙungiyar fasaha ce ta farar hula da ke sa ido da bayyana gaskiyar bayanai game da kasafin kuɗi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya bayyana cewa 'yan majalisa sun cusa ayyuka 11,122, wanda ya kai kashi 12.5% na jimillar kasafin Naira tiriliyan 54.99 da aka sanya hannu a kai.

Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin 2025 na Naira tiriliyan 49.7 a watan Disamba, 2024, wanda ake sa ran zai daidaita tattalin arziki, rage talauci, ƙarfafa tsaro da haɓaka ci gaba.

A watan Fabrairu 2025, shugaba Tinubu ya ƙara yawan kasafin zuwa Naira tiriliyan 54.2 saboda samun karin kudaden shiga daga hukumar FIRS, Kwastam da sauransu.

Ya sanya hannu kan kasafin karshe na N54.99 tiriliyan a ranar 28 ga Fabrairu, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Tiriliyoyin Naira da ake zargin an cusa a kasafin

Sai dai binciken BudgIT ya nuna cewa babban kaso na ƙarin ya fito ne daga ƙarin ayyukan da majalisar ta saka bisa son rai.

Rahoton ya nuna cewa an saka ayyuka 238 da kowanne kudinsa ya haura Naira biliyan 5, wanda darajarsu gaba daya ta kai Naira tiriliyan 2.29.

Haka nan, kungiyar ta ce an sanya ayyuka 984 da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 1.71 da wasu ayyuka 1,119 da kudinsu ya ke tsakanin Naira miliyan 500m zuwa Naira biliyan 1.

Sauran ayyukan da BudgIT ke zargin 'yan majalisar sun cusa a kasafin na 2025 sun hada da:

  • Ayyukan mazabu 3,573 da kudinsu kai N653.19bn
  • Ayyukan mazabun sanatoci 1,972 da darajarsu ta kai N444.04bn
  • Sanya fitilun titi 1,477 da darajar aikin ta kai N393.29bn
  • Gina famfunan tuka tuka guda 538 da darajarsu ta kai N114.53bn
  • Ayyukan ICT 2,122 da darajarsu ta kai N505.79bn
  • Naira biliyan 6.74 na “karfafa sarakunan gargajiya”

Ma'aikatun da ake zargin an cusawa ayyukan bogi

BudgIT ta ce yawancin wadannan ayyuka ba su da alaka da ainihin burin ci gaban kasa, abin da ke kara nuna rashin gaskiya karara a harkar tafiyar da kudaden jama'a.

Rahoton ya ce ma’aikatar noma ce ta fi samun ƙarin kuɗin ayyukan, daga N242.5bn zuwa N1.95trn bayan majalisa ta saka ayyuka 4,371 da darajarsu ta kai N1.72trn.

Haka zalika, ana zargin ma’aikatar kimiyya da fasaha ta samu ƙarin N994.98bn, yayin da ma'aikatar tsare-tsare da tattalin arziki ta tashi da N1.1tr.

BudgIT ta kuma caccaki wasu ma’aikatu da hukumomi (MDAs) bisa gudanar da ayyuka da ba sa cikin ayyukansu na doka.

Misali, ta ce an ware wa cibiyar keere-keren kayan aikin gona (NCAM) da ke Ilorin, jihar Kwara, N400m don tallafin karatu da N350m don inshorar lafiyar al’umma a Bayelsa ta Yamma, lamarin da ya sha bamban da aikinta na asali.

Majalisar dattawa ta yi martani kan rahoto da kungiyar BudgIT ta fitar
Zauren majalisar dattawa yayin da ake zaman majalisar kamar yadda aka saba. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Majalisar dattawa ta yi wa BudgIT martani

A martanin da majalisar dattawa ta mayar, mai magana da yawunta, Sanata Yemi Adaramodu, ya musanta duk zarge-zargen, yana kiran rahoton da “aikin waɗanda ke yada ƙarya da raba kan al’umma.”

Jaridar Leadership ta ruwaito Sanata Yemi yana cewa:

“An gabatar da kasafin 2025 daga bangaren zartarwa, kuma majalisar taraya ta amince da shi ne kamar yadda aka kawo shi.
“Waɗanda ke neman tayar da zaune tsaye a tsakanin jama’a da majalisar tarayya su ne ke yada rahotanni marasa tushe.”

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, majalisar wakilai ba ta fitar da wata sanarwa ba tukuna kan batun.

Kasafin 2025: Tinubu zai kashe N55bn kan jirage

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 55 domin kula da rukunin jiragen fadar shugaban kasa a kasafin kudin 2025.

Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyun adawa sun bayyana wannan yunkuri a matsayin abin da bai dace da bukatun talakawa a wannan lokaci ba.

Kungiyoyin fararen hula da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun yi kira ga gwamnati da ta sake duba lamarin, duba da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.