2027: A karshe, Ganduje Ya Tono Sirrin da ke Saka 'Yan Adawa Shiga APC

2027: A karshe, Ganduje Ya Tono Sirrin da ke Saka 'Yan Adawa Shiga APC

  • Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce PDP na ta shiga mummunan yanayi sakamakon samun cikas da rikice-rikice a cikin gida
  • Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa hakan ne ke tilasta wa ɗimbin ƴan jam’iyyar hamayya sauya sheƙa zuwa APC a sassan ƙasar nan
  • Ganduje ya ce nasarorin APC a zaɓukan baya da shirin da take na gaba ne ke janyo hankalin ƴan siyasa daga PDP da LP zuwa cikinta a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP da ke hamayya a ƙasa na cikin wani hali na karancin ƙarfi da rikice-rikice.

Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa hakan ke sa mambobinta sauya sheƙa zuwa APC domin samun mafita.

Ganduje
Ganduje ya ce siyasa na kokarin karewa PDP. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa Ganduje ya bayyana haka ne yayin taron APC da aka gudanar a fadar shugaban kasa, inda aka tattauna nasarorin jam’iyyar da kuma shirin ta na gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya ce APC na ci gaba da faɗaɗa karfinta a fadin ƙasar, tare da samun sababbin mambobi daga manyan jam’iyyun hamayya da suka haɗa da PDP da LP.

Ganduje: 'Dalilin da ya sa 'yan PDP komawa APC'

A cewar Ganduje, rikice-rikice da fitar jiga-jigai daga jam’iyyar PDP na nuna yadda jam’iyyar ke fama, abin da ke nuna karancin jagoranci da dabarun siyasa a cikin jam’iyyar.

The Guardian ta rahoto Ganduje ya ce:

“PDP yanzu na fama da matsala sosai saboda rikicin cikin gida da ficewar mambobi, kuma wannan ne ya sa mutane da dama daga cikinsu ke komawa APC.”

Ganduje ya jaddada cewa APC na da gwamnonin jihohi 22 daga cikin 36 a Najeriya, kuma akwai wani gwamna da ke shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar a makonni masu zuwa.

APC na shirin samun karin nasarori inji Ganduje

Ganduje ya ce jam’iyyar na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓukan da ke tafe a wasu jihohi kamar Anambra da kuma babban zaɓen 2027.

Ganduje
Ganduje ya ce suna shirin karbar wani gwamna daga jam'iyyar adawa. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Ya ce zaɓukan da aka yi a wasu jihohi bayan babban zaɓen 2023 sun nuna cewa jam’iyyar na ƙara karɓuwa a zukatan ƴan Najeriya, kuma APC na shirin ƙara samun rinjaye a matakai daban-daban.

Ganduje ya buƙaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da hada kai, su guji rikici domin tabbatar da dorewar nasara da cigaban jam’iyyar a matakin ƙasa da jihohi.

APC ta ce tana lale maraba da gwamna Fubara

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce za ta yi aiki tare da gwamna Simi Fubara.

Shugaban APC na jihar Rivers ya ce ba abin da zai hana jam'iyyar karbar Fubara da mika masa ragama idan ya dawo cikinsu.

Ya kuma bayyana cewa akwai bayanan da ba za su ba gwamnan ba saboda yana adawa da su, amma da zarar ya sauya sheka za su fada masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng