Sabuwar Rigima: Akpabio Ya Maka Natasha a Kotu kan Yi Masa 'Rashin Kunya'
- Godswill Akpabio, ya bukaci kotun tarayya ta umurci Natasha Akpoti-Uduaghan da ta goge wani sakon barkwanci da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta
- Shugaban majalisar dattawan ya ce sakon da Sanata Natasha ta wallafa ya saba wa umarnin kotu, yana kuma neman ta ba shi hakuri a jaridu biyu na kasa
- Sanata Natasha ta wallafa sakon ne a ranar 27 ga Afrilu 2025, tana mai sukar salon shugabancin Akpabio da abin da ta kira da rashin gaskiya a majalisar dattawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An koma kotu a wani sabon rikici da ke tsakanin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da Natasha Akpoti-Uduaghan.
Sanata Godwill Akpabio ya shigar da wata bukata a gaban kotu domin dakile abin da ya kira da bata masa suna da Sanata Natasha ta yi.

Asali: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa Akpabio ya nemi kotun tarayya da ke Abuja da ta tilasta wa Sanata Natasha ta goge wani sako da ta wallafa a Facebook game da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan Akpabio, Kehinde Ogunwumiju ya bayyana cewa sakon ya ci karo da wani umarnin da kotu ta bayar a halin da ake ci gaba da sauraron karar da Akpoti ta shigar.
Me sakon Natasha ga Akpabio ya kunsa?
A ranar 27 ga Afrilu, Akpoti ta wallafa wani sako da ta kira na barkwanci a shafinta na Facebook, tana mai cewa tana ba da hakuri kan “laifinta na kiyaye mutunci da darajarta.”
A cikin sakon, ta yi ishara da cewa a karkashin shugabancin Akpabio, nasara a majalisar dattawa ba ta dogara da cancanta ko kwarewa ba, illa dai bin ra’ayi da tsarin son kai.
Sakon Natasha ya yadu a kafafen sada zumunta inda mutane da dama suka rika tofa albarkacin bakinsu.
Wasu na ganin sakon wata irin hanya ce ta nuna rashin amincewa da dakatarwar da aka yi mata, yayin da wasu ke ganin hakan ya sabawa umarnin kotu.
Akpabio ya bukaci Natasha ta ba shi hakuri
The Guardian ta rahoto cewa a cikin bukatun da ya gabatar a gaban kotu, lauyan Akpabio ya nemi Akpoti-Uduaghan ta ba da hakuri kai tsaye a jaridu biyu na kasa.
Rikicin tsakanin shugabannin biyu ya samo asali ne tun watan Fabrairu, bayan wata cacar baki da ta faru kan tsarin zama a majalisa, lamarin da ya kai ga dakatar da Akpoti a watan Maris.
Tun daga lokacin, bangarorin biyu na ci gaba da shari’a da juna, inda kowanne ke neman diyyar makudan kudi saboda abin da ya kira da bata suna da cin mutunci.

Asali: Facebook
Akpabio ya kafa kwamiti kan rikicin Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya kafa kwamiti domin lura da shugaban riko na jihar Rivers.
Bayan dawowa daga hutun majalisa, Godswill Akpabio ya ce kwamitin zai saka ido kan yadda shugaban rikon ke jagorantar jihar.
A nata bangaren, majalisar wakilai ta ce za ta hada kai da majalisar dattawa wajen kafa kwamitin sulhu da zai warware rikicin Rivers.
Asali: Legit.ng