Natasha Ta Barowa Akpabio Aiki a Wasikar 'Ba da Hakuri' da Ta Rubuta Masa

Natasha Ta Barowa Akpabio Aiki a Wasikar 'Ba da Hakuri' da Ta Rubuta Masa

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta rubuta wasikar "ba da hakuri" ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan zargin da ta yi masa
  • Wasikar cike take da shakiyanci da izgili, tana nuna cewa har yanzu tana tsaye kan ikirarin da ta yi a baya na cewa ya nemi yin lalata da ita
  • Rahotanni sun nuna cewa Natasha Akpoti ta rubuta wasikar ne yayin da Akpabio ke birnin Rome domin jana'izar marigayi Fafaroma Francis

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar a majalisa, ta fitar da wata wasika da take cewa tana ba da hakuri ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Sai dai hakurin da ta bayar na kunshe da shagube ne da kuma nuna rashin yarda da salon shugabancinsa, lamarin da ya sake janyo ce-ce-ku-ce a cikin al’umma.

Natasha
Natasha ta yi wa Akpabio shagube cikin wasikar ba da hakuri. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Twitter

Legit ta tattaro abubuwan da Sanata Natasha ta fada ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta wallafa cewa cewa Akpabio yana birnin Rome domin halartar jana'izar marigayi Fafaroma Francis, yayin da wasikar Natasha ta bayyana ga manema labarai a Abuja.

Abubuwan da waskikar natasha ta kunsa

A cikin wasikar da Sanata Natasha ta rubuta ta yi ba'a ga Godswill Akpabio kan bukatar neman ba shi hakuri:

Wani sashe na wasikar ya bayyana cewa:

"Mai girma shugaban majalisa Godswill Akpabio, cikin nadama nake ba da hakuri saboda babban laifin da na aikata na kare mutunci na a gaban ka."

Ta ce bayan dogon nazari, ta fahimci cewa ba bisa cancanta ake samun amincewa a majalisa ba, sai ta hanyar biyan bukatun wasu da faranta musu rai.

Natasha ta kara da cewa rashin amincewarta da nema lalata da ita ya zama karya dokokin da wasu shafaffu da mai suka kafa da kansu, maimakon dokokin kasa.

Ta ce tana rokon Akpabio da ya yafe mata saboda laifin tunanin cewa ta samu kujerarta a majalisa ne ta hanyar zabe ba ta neman lalata ba.

Natasha ta kammala da cewa:

"Zan cigaba da kasancewa kamar yadda nake, ba gudu ba ja da baya, ba kuma jin tsron kowa,'

Wasikar da Natasha ta fitar ta sake tayar da kura, inda da dama ke kallon cewa rikicin da ke tsakaninta da Akpabio zai dauki lokaci kafin ya lafa.

Ana ganin cewa wannan sabon salo da Natasha ta dauka yana kara jan hankali a siyasar Najeriya, musamman kan batun ‘yancin mata da adalci a shugabanci.

Natasha
Natasha ta ce za ta cigaba da gwagwarmaya. Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Twitter

A yanzu haka dai an zuba ido domin ganin ko wasikar da Natasha ta rubuta za ta jawo mata matsala da shugabancin majalisa ko a'a.

Yadda aka kai harin gidansu Natasha

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti ta bayyana halin da aka shiga yayin da aka kai hari gidansu a jihar Kogi.

Natasha Akpoti ta bayyana cewa an kai harin ne a lokacin da wani dan uwanta ya ziyarci jihar domin duba wasu ayyukan da take yi a mazabarta.

Sanatar ta yi zargin cewa maharan sun yi tunanin cewa ita da kanta ne ta ziyarci gidan sai suka kai hari domin kawo karshen rayuwarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng