Dangote Ya Fadi Abin da Kamfanin Simintinsa ke Tsakurawa Gwamnatin Tarayya

Dangote Ya Fadi Abin da Kamfanin Simintinsa ke Tsakurawa Gwamnatin Tarayya

  • Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya ce gwamnatin tarayya na cin gajiyar harkokin kamfaninsa fiye da yadda ake zato
  • Ya bayyana haka ne a babban taron 'yan kasuwa da ya gudana a jihar Taraba, inda ya bayyana irin tagomashin da ake samu a kamfanin simintinsa
  • Dangote ya shawarci gwamnati a kan bunkasa tattalin arziki, ya ce ana samun ci gaba mai ɗorewa idan aka tallafa wa kamfanoni masu zaman

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Taraba – Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na samun kwabo 52 daga kowanne N1 da ake samu daga simintin da kamfanin ya sayar.

Ya bayyana hakan ne a taron zuba jari na kasa da kasa da aka gudanar a jihar Taraba a ranar Laraba, 21 ga watan Mayu, 2025, wanda manyan yan kasuwa suka halarta.

Dangote
Dangote ya fadi kudin da gwamnati ta ke samu a kamfaninsa Hoto: Dangote Foundation
Asali: Getty Images

The Cable ya wallafa cewa taken taron shi ne: “Buɗe damammakin zuba jari na Taraba: Inganta noma, makamashi, hakar ma’adinai da masana’antu domin ci gaba mai ɗorewa.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya magantu kan bunkasa tattalin arziki

Jaridar The ICIR ta ruwaito cewa Dangote ya ce taron ya zo a daidai lokacin da ya kamata, ganin yadda ya mayar da hankali kan buɗe ƙofofin jari da bunƙasa tattalin arzikin jihar.

A cewarsa:

“Zan tabbatar muku abu mai matuƙar ban mamaki, amma gwamnatin tarayya – ba ma na jiha ba – ita ke samun mafi yawan riba daga harkar simintinmu."
"Domin daga kowanne Naira guda da muka samu, kashi 52 na tafi zuwa gwamnati.”

Dangote: ‘Gwamnati na samun kudin shiga’

Dangote ya jaddada cewa gwamnati na amfana da zuba jari matuƙar ta samar da kyakkyawan yanayi da zai ba yan kasuwa damar aiki da biyan haraji yadda ya dace.

Dangote
Aliko Dangote ya ce akwai bukatar a karfafawa yan kasuwa Hoto: Dangote Industries
Asali: Facebook

A cewarsa:

Kun taɓa jin cewa gwamnatin Amurka na da rijiyar man fetur? A'a. Gwamnatin Amurka ba ta da rijiyar man fetur, duk da cewa su ne manyan masu samar da man fetur a duniya. Amma kuɗin su na haraji suke samu.”

Dangote ya bayyana cewa idan gwamnati ta ƙarfafawa yan kasuwa masu zaman kansu suka zuba jari, hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga al’umma.

A cewarsa:

“Shugabannin siyasa suna da alhakin cika alkawurra da suka ɗauka. Idan suka yi alkawarin samar da ayyukan yi, ai ba su da masana’antu.
Ba su a cikin harkar kasuwanci. Ba su da banki, masana’antu ko wani abu makamancin haka. Don haka, hanya ɗaya da za su iya samar da arziki da ci gaba ita ce ta hanyar ɓangaren masu zaman kansu.”

Dangote ya nanata cewa ɓangaren masu zaman kansu ne ke ɗauke da nauyin bunƙasa tattalin arziki, yayin da ya nemi haɗin kai daga gwamnati domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Taraba: Dangote ya yi alkawarin zuba jari

A baya, mun wallafa cewa Shahararrun ‘yan kasuwa Aliko Dangote da Tony Elumelu sun bayyana shirinsu na zuba jari a jihar Taraba, musamman a bangarorin noma da makamashi.

Sun bayyana haka ne a yayin taron kasuwanci da aka gudanar a jihar, inda suka ce za su zuba hannun jarin ne domin tallafa wa tattalin arzikin jihar da kuma bunkasa Najeriya baki ɗaya.

Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arziki, ciki har da Dangote da Elumelu, suka jaddada bukatar ƙarfafa yan kasuwar cikin gida da waje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.