Dangote Ya Gayawa Gwamnatoci Hanyar Jawo Masu Zuba Hannun Jari daga Waje
- Alhaji Aliko Dangote ya halarci taron da aka shirya kan zuba hannun jari a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
- Hamshaƙin attajiran ya yi amfani da taron wajen ba gwamnatoci shawara kan hamyar nemo masu zuba hannun jari daga waje
- Dangote ya bayyana cewa ba da fifiko ga masu zuba hannun jari na cikin gida zai sanya tattalin arziƙin ƙasar nan ya haɓaka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ba gwamnatocin tarayya da na jihohi shawara kan jawo masu zuba hannun jari.
Aliko Dangote ya shawarci gwamnatocin da su ba masu zuba hannun jari na cikin gida fifiko domin haɓaka tattalin arzikin ƙasa.

Asali: Getty Images
Ya bayar da wannan shawara ne a wajen taron zuba hannun jari na Taraba da aka gudanar a Jalingo, wanda ya jawo hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje, cewar rahoton Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote ya nuna muhimmancin zuba jari
Hamshaƙin attajirin na ɗaya a Afirka ya bayyana cewa masu zuba hannun jari na cikin su ne ke jawo hankalin masu zuba jari daga waje, domin babu wani ɗan kasuwa daga ƙasashen waje da zai zo zuba jari a ƙasar da kasuwancin cikin gida bai bunƙasa ba.
“Ina so na bayar da wata shawara, mai girma gwamna. Hanya guda ɗaya ta jawo hankalin masu zuba hannun jari daga waje ita ce ta samun masu zuba hannun jari na cikin gida. Su ne ainihin masu jawo masu zuba hannun jari daga waje."
"Idan ba ka gayyaci masu zuba jari na cikin gida su zuba jari ba, babu wani ɗan waje da zai zo. Sai dai idan sun ga cewa akwai damar zuba jari. Idan sun ga abubuwa na tafiya daidai, ba sai an gayyace su ba, su da kansu za su zo."
- Aliko Dangote
Dangote ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na samun riba mai yawa daga kamfanin simintin Dangote, inda ya ce cikin kowace Naira ɗaya da kamfanin ya samu, kobo 52 na zuwa hannun gwamnatin tarayya.
"Na tabbata zai ba ku sha’awa ku ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya, ba ma jiha ba, ita ce ke cin riba mafi yawa daga, alal misali, harkar simintinmu."
"Domin a kowace N1 da muka samu, kobo 52 yana zuwa ga gwamnatin tarayya. Wannan shi ne amfanin hakan. Idan gwamnati ta sauƙaƙawa mutane, za su iya kafa kasuwanci. Dole ne mu bi doka, mu biya haraji."
- Aliko Dangote

Asali: Getty Images
Dangote ya ba gwamnati shawara
Dangote ya ƙara da ƙarfafa gwiwar gwamnati da ta ci gaba da ƙarfafa zuba hannun jari, musamman na cikin gida, yana mai cewa hakan ne kawai zai samar da ayyukan yi.
“Ina roƙon cewa gwamnati ta ci gaba da ƙarfafa zuba hannun jari, musamman na cikin gida. Idan aka ƙarfafa, zuba jari zai ƙaru. Idan ba a ƙarfafa ba, ba za a sami ayyukan yi ba."
- Aliko Dangote
Aliko Dangote ya shiga jerin masu taimako
A wani labarin kuma, kun ji cewa hamshaƙin attajirin nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya kafa tarihi.
Dangote ya shiga cikin jerin attajirai 100 na duniya masu amfani da dukiyarsu wajen taimakon bayin Allah.
Hamshaƙin attajirin shi ne ɗan Najeriya ɗaya tilo da ya shiga cikin jagororin guda 100 da suka samu shiga cikin jerin.
Asali: Legit.ng