Cushen Kasafi: An Gano N206 Ta Mecece Da Aka Ganta A Jaddawalin Ma'aikatar Jin Ƙai

Cushen Kasafi: An Gano N206 Ta Mecece Da Aka Ganta A Jaddawalin Ma'aikatar Jin Ƙai

  • A satin Da ya gabata ne Ministarn Wal-wala Da Jinkai Ta Sanar Da Cewa An Mata Cushe A Kasafin Kudinta
  • Majalissar Dattijai Ta Fara Jin Ta Bakin Ma'aikatu Da Hukumomin Gwamnati Kan Kare Kasafin Kudin Su Na Shekarar 2023
  • Wannan Kasafin Kudin Na Shekarar 23023 shine dai kasafi mafi yawa da Nigeria ta Gabatar Wanda ya Doshi Tiriliyan 18 da doriya

Abuja : Naira biliyan 206 da aka sanya a boye a cikin kasafin kudin ma’aikatar Walwala da Jinkai, ya bayyana cewa an sanya kudin ne da gangan, domin sayen makamai da kayan aikin sojoji.

Wannan ya fito ne lokacin da Majalisar Dattawa ta gano cewa kasafin kudin ma'aikatar ya samu wani bakon kudi har Naira biliyan 206 da aka kara ba tare da cikakken bayani ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Aike Da Dalibin Aminu Gidan Kurkuku Bisa Zargin Cin Zarafin Uwar Gidan Buhari

Sadiya Umar-Farouq, ta bayyana mamakin gano abin da majalisar dattawa ta yi, lokacin da aka nemi ta yi bayanin kasancewar makudan kudade a cikin kasafin kudin ma’aikatar ta.

Sadiya ta bayyanawa majalissa cewa:

“Eh, a cikin kasafin kudin mu mun tabo maganar ayyukan 2022 na Hukumar kula da yankin ci gaban arewa maso gabas wato NEDC ne wanda basu aiwatar dasu ba, suma mu kara sanyawa a cikin daftarin. sannan akwai kudaden da ba'a bamu ba dag asusun gwamnati. Sannan akwai kuma kudaden da aka sanya su domin a biya wasu aiyukan, amma ba'a biya ba mun sake sa su suma a cikin kasafin”

A wani rahoto da kafar Leadership ta rawaito tace ministan tace itama tayi mamaki yadda taga kudi kusan naira biliyan 206 a ciki kuma akai ikirarin na siyan makamai ne da kayan sojoji, kuma wai a ma'aikatar jinkai, to ai lamari ya lalace, inji Sadiya.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta Fito a Kan Zargin Cusa N1.7tr da Minista Tayi a Kasafin kudin Shekarar 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shi ya sa na ce ba zan ce komai a kai ba har sai mun samu karin haske daga ma’aikatar kudi. Idan da a ce mun nemi Naira biliyan 206 don wani aiki na daban, to da sai muce eh yana cikin lissafin kasafin kudinmu".

Shi ma babban sakataren ma’aikatar Sani Gwarzo ya bayyana yadda aka samu naira biliyan 206 a cikin kasafin su a matsayin wani kuskure da ya kamata a binciki ma'aikatar kudi kan kan wannan batu.

"A matsayin hanyar da za mu fahimci tushen wannan batu, muna kira ga majalisar dattawa da ta yi watsi da duk wani abu ko kokarin tabbatar da ’yan Najeriya cewa ma’aikatar wal-wala da jinkai bata cikin wannan batu na kari a cikin kasafin kudinta
Sadiya
Cushen Kasafi: An Gano N206 Ta Mecece Da Aka Ganta A Jaddawalin Ma'aikatar Jin Ƙai Hoto: Leadership
Asali: UGC

"Yana da kyau gwamnati tayi tsari mai kyau na yakar cin hanci da rashawa a tsakanin hukumomin gwamnati da kuma bin diddigin yadda suke kashe kudaden su wanda suka sanya a kasafi".

Kara karanta wannan

Sojin Nigeria Sunyi Nasarar Kashe Shugaban ISAWP A Nigeria, Bayan Wani Hari Da Suka Kai

Buhari Yaddamar Da Kasafin Kudi

A kasafin kudin da shugaban Muhammadu Buhari ya gabatar gaban hadakar zauran majalisar kasar da wasu ministocinsa, wanda yakai tiriliyan 18.6, a matsayin kasafin kudin shekarar 2023

Shugaban ya ware naira tiriliyan 1.35 domin shawon kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan musamman ma yankin arewa maso yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel