BudgIT Ta Bankado Ayyukan N6.9trn da Majalisa Ta Cusa a Kasafin Kudin 2025

BudgIT Ta Bankado Ayyukan N6.9trn da Majalisa Ta Cusa a Kasafin Kudin 2025

  • Wani bincike ya bankado karin ayyuka 11,122 da darajarsu ta kai N6.93tn da aka saka a kasafin kudin 2025 ba tare da an fitar da bayanin dalilin hakan ba
  • Kungiyar BudgIT, wajda ta gudanar da binciken, ta ce an gano cewa an yi wannan karin ne karkashin wasu ma’aikatun gwamnati, ciki har da Ma’aikatar Noma
  • BudgIT ta ce akwai bukatar tsari mai inganci don bin diddigin kasafin kudi da tabbatar da cewa an aiwatar da shi bisa ka’ida da dokar kasa a majalisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wata kungiya mai zaman kanta da ke sa ido kan kasafin kudi, BudgIT, ta ce ta gano karin ayyuka da aka saka a kasafin kudin 2025 da Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da shi.

Kungiyar ta bayyana a ranar Talata cewa ta gano ayyuka 11,122 da darajarsu ta kai Naira tiriliyan 6.93 da aka saka a cikin kasafin kudin 2025 ba tare da bayani ba.

Tinubu
BudgIT ta ce an yi cusen ayyuka a kasafin kudin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Rahoton da kungiyar ta wallafa a shafinta na X ya nuna cewa wannan kaso na ayyuka da aka saka ba bisa ka’ida ba ya kai 12.5% na jimillar kasafin kudin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Disamba 2024 ne Shugaba Tinubu ya mika kasafin kudi na Naira tiriliyan 49.7 ga shekarar kudin 2025 ga Majalisar Dokoki ta kasa.

BudgIT: An yi karin ayyuka a kasafin kudi

Daily Trust ta ruwaito cewa a watan Fabrairu 2025, Shugaban kasa ya nemi a kara masa kasafin daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2.

A ranar 13 ga Fabrairu, Majalisar Dokoki ta amince da sabon kasafin kudi da ya kai Naira tiriliyan 54.99, inda aka kara Naira biliyan 700 daga abin da shugaban ya nema.

Cikakken binciken BudgIT ya nuna cewa akwai ayyuka 238 da kowannensu ya haura Naira biliyan 5, jimillarsu Naira tiriliyan 2.29, da aka saka cikin kasafin kudin ba tare da bayani ba.

Rahoton ya ce:

“Haka zalika, an saka ayyuka 984 da darajarsu ta kai Naira tiriliyan 1.71 da kuma ayyuka 1,119 da ke tsakanin Naira miliyan 500 zuwa biliyan 1, jimillar su Naira biliyan 641.38, ba tare da an bi ka'ida ba."

Kare-karen da aka yi a kasafin kudin 2025

Bincike ya kuma gano cewa an ware ayyuka 3,573 da darajarsu ta kai Naira biliyan 653.19 ga mazabu, yayin da aka bai wa yankunan Sanatoci ayyuka 1,972 da kudinsu ya kai Naira biliyan 444.04.

Har ila yau, an gano ayyuka da dama da ba a amince da su ba da suka hada da sanya fitilun titi 1,477 da darajarsu ta kai Naira biliyan 393.29, da kuma gina rijiyoyi 538 da kudinsu ya kai Naira biliyan 114.53

Tinubu
BudgIT na son Tinubu ya bi diddigin kasafin kudin bana Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Sai kuma ayyukan fasahar sadarwa (ICT) guda 2,122 da darajarsu ta kai Naira biliyan 505.79 da bayar da tallafi ga sarakunan gargajiya da darajarsa ta kai Naira biliyan 6.74

A cewar rahoton:

“Abin mamaki, 39%na dukkanin wadannan ayyuka da aka saka—wadanda suka kai 4,371 da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 1.72—an cusa su ne a kasafin Ma’aikatar Noma, wanda hakan ya kara yawan kasafin ma’aikatar daga Naira biliyan 242.5 zuwa tiriliyan 1.95.”

BudgIT ta bukaci Shugaba Tinubu da ya tabbatar da cewa kasafin kudi na kasa ya dace da tsare-tsaren cigaban kasa na matsakaici da dogon lokaci.

Kungiyar ta bayyana cewa:

“Ko da yake ana ta rade-radin cewa Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai suna karbar Naira biliyan 1 da 2 don ayyukan mazabu, bincikenmu ya nuna cewa kason da ake ba su ya haura haka."

Tinubu ya gabatar da kasafin kudin Abuja

A baya mun wallafa cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kudin Naira tiriliyan 1.78 na babban birnin tarayya ga Majalisar Dokoki ta Kasa don amincewarsu.

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta wasikar shugaban kasa a zauren majalisar, inda Tinubu ya ce amincewa da kasafin cikin gaggawa zai taimaka sosai.

A cewar Shugaba Tinubu, kasafin kudin zai bai wa gwamnati damar gudanar da manyan ayyukan da za su inganta rayuwar mazauna babban birnin tarayya, Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.