Rusau Ya Zo da Tangarda a Kano bayan Jami'an Tsaro Sun Harbe Mutane
- Rushe gidajen mutane ya bar baya da ƙura a jihar bayan Kano bayan an samu asarar rayukan mutum huɗu
- Lamarin dai ya auku ne a Rimin Auzinawa wanda yake cikin ƙaramar hukumar Ungogo ta jihar Kano a daren yau
- Majiyoyi sun bayyana cewa jami'an tsaro sun buɗe wuta kan mutanen da suka ƙi a amincewa a rushe gidajensu
- Abin ya faru ne a wani fili da ake taƙaddama a kansa tsakanin mahukuntar jami'ar BUK da kuma wasu mutanen gari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - An samu asarar rayukan mutane huɗu sakamakon rikici kan rushe gine-gine a jihar Kano.
Lamarin dai ya auku ne a garin Rimin Auzinawa, ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami’an tsaro ne suka harbe mutanen bayan da mazauna yankin suka mayar da martani kan rushe gidajensu.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki da wasu mutane 5, sun kashe mutum 1 daga ciki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rushe gine-ginen mutane a Kano
Majiyoyi sun bayyana cewa hukumar KNUPDA ta taɓa yin alamar rusau ga gine-ginen da aka rushe, waɗanda galibi gidaje ne kusan guda 40 da ake aikin ginasu.
Filin dai da ake taƙaddama kansa mallakar jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ne.
Wani mazaunin yankin wanda abin ya shafa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce KNUPDA ta taɓa tabbatar musu cewa gine-ginensu ba a cikin filin BUK suke ba.
"Mun warware matsalolinmu da KNUPDA, sun tabbatar mana cewa filinmu ba na jami’ar BUK ba ne. Amma da daddare a ranar Lahadi, jami’an KNUPDA da jami’an tsaro sun zo suka rushe gidajen."
"Lokacin da mutane suka nuna rashin amincewa, jami’an tsaro sun buɗe wuta inda suka kashe mutane huɗu, waɗanda aka riga aka birne. Wannan abu ne mai ban takaici."
- Wata majiya
Me hukumomin Kano suka ce kan lamarin?
Ƙoƙarin jin ta bakin hukumar KNUPDA ya ci tura domin ba a samu shugaban hukumar ba.
Lokacin da aka ziyarci ofishin KNUPDA, an tarar kusan babu mutane, wani ma’aikaci ya ce jami’an hukumar sun ƙauracewa ofis ɗin ne saboda tsoron ramuwar gayya.
"Akwai tashin hankali ofis ɗin. Hakan ya sanya babu motoci a wurin ajiyesu, babu manyan jami’ai, sai ƙananan ma’aikata, kuma babu wani umarni kan abin da za a yi."
- Wani jami’in hukumar KNUPDA
Sai dai, wani babban darakta a KNUPDA, wanda shi ne kadai babban jami’in da ke ofis a lokacin, ya musanta cewa KNUPDA ce ta rushe gine-ginen.
Ya bayyana cewa wata tawaga ce daga ma’aikatar filaye tsare-tsaren birane ta jihar Kano ta ɗauki matakin rushe gine-ginen.
Wani jami’i daga ma’aikatar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar cewa filin na BUK ne kuma ya ce gwamnati za ta fitar da sanarwa a hukumance nan ba da dadewa ba.
Ƴan sanda sun cafke masu shirin tayar da bam
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sanda a jihar Kano sun samu nasarar cafke wasu mutane da suka yi shirin tayar da bam, yayin mauludin Tijjaniyya a Kano.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro sun nuna kwarewa, sun ceto mutanen da 'yan bindiga suka sace a Kaduna
Jami'an ƴan sandan dai sun yi caraf da mutanen ne a jajibirin bikin mauludin wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke cikin birnin Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng