Kano: NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Fitaccen Matashi Mai Safarar Kwayoyi, Ya Shiga Hannu
- Hukumar NDLEA ta shigar da kara kan wani matashi Sulaiman Danwawu a gaban kotun tarayya a Kano kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi
- An kama shi matashin da miyagun kwayoyi da suka hada da Tramadol, Rohypnol da Pregabalin, dukkaninsu na kamanceceniya da hodar iblis
- NDLEA ta ce ta kuma bayyana cewa ana yiwa Sulaiman Danwuwu tuhume-tuhume takwas, dukkaninsu a kan safarar kwayoyi masu hadari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta gurfanar da wani fitaccen mai safarar kwaya a Kano, Sulaiman Danwawu, a gaban babbar kotun tarayya.
A ranar 10 ga Mayu, rundunar ‘yan sandan Kano ta bayyana cafke Sulaiman Danwawu da wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin jihar.

Asali: Facebook
Bayan kama shi, Daily Nigerian ta ruwaito cewa an mika Danwawu ga hukumar NDLEA domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban kotu bisa safarar miyagun kwayoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da NDLEA ke yi wa Sulaiman Danwawu
Rahoton ya ce hukumar NDLEA ta shigar da kara a kotu kan zargin Sulaiman Danwawu mallakar nau’o’in miyagun kwayoyi daban-daban da ba bisa ka’ida ba.
A cikin karar da hukumar ta shigar, an ce:
“Kai SULAIMAN AMINU, namiji, mai shekara 37, a ranar 8 ga Mayu, 2025, a titin Cairo, Tudun Yola, karamar hukumar Gwale, Jihar Kano, an kama ka da Tramadol mai nauyin girman 72, wata kwaya da ta yi kama da hodar iblis ba tare da izini ba, wanda hakan laifi ne da ya saba sashi na 19 na dokar NDLEA, Cap N30, Dokokin Tarayyar Najeriya, 2004.”
Danwawu: Sauran zarge-zargen NDLEA
Hukumar ta NDLEA ta kuma zargi Danwawu da mallakar wasu kwayoyi masu illa da suka hada da giram 1.7 na Rohypnol, kilogiram 24.1 na Pregabalin da sauran miyagun kwayoyi.
Hukumar ta ce dukkannin wadannan kwayoyi ana sarrafa su ne ba bisa ka’ida ba, kuma laifuffuka ne da suka saba wa dokar NDLEA, wanda hukunci ya hau kansa karkashin Sashe na 19 na dokarsu.

Asali: Twitter
A cewar NDLEA, fitaccen matashin yana fuskantar tuhume-tuhume guda takwas – dukkanninsu na da nasaba da safarar miyagun kwayoyi masu hadari da ga jama'a.
NDLEA ta cafke mai safarar miyagun kwayoyi
A wani labarin, mun wallafa cewa Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta dakile wani yunkuri na safarar hodar iblis daga Najeriya zuwa Iran.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce an cafke Ihensekhien Miracle Obehine a filin jirgin sama na kasa da ke Fatakwal, lokacin da take shirin hawa jirgin Qatar Airways zuwa Iran.
Femi Babafemi, daraktan hulda da jama’a na NDLEA a Abuja, ya ce Obehi ta ɓoye kullin hodar iblis guda uku a al'aurarta, ta hadiye kwayoyi 67 sannan ta sa wasu guda biyu a jakarta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng