NDLEA Ta Yi Ram da Matar da Ta Boye Hodar Iblis a Al'aura da wasu Sassan Jikinta
- Wata mata mai suna Ihensekhien Miracle Obehi ta shiga hannun jami’an NDLEA a filin jirgin sama na kasa da kasa da ke Fatakwal da ke jihar Ribas
- An cafke ta tana kokarin safarar miyagun kwayoy da suka hada da hodar iblis da ta boye a cikin al'aurarta da zunduma hijabi don kaucewa jam'an tsaro
- Haka kuma matar ta nuna karfin hali, inda aka gano ta hadiye kullin hodar guda 67, wanda ta shafe kwanaki ta na kasayar da su a hannun NDLEA
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers – Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun dakile yunkurin wata mata, Ihensekhien Miracle Obehi, mai ƙoƙarin safarar kwayoyi zuwa Iran.
Misis Obehi ta ɓoye kwayoyi masu yawa na nau’in hodar iblis a matuncinta, cikinta da kuma ƙasan jakarta, bayan ta zunduma hijabi don kaucewa binciken jami'an tsaron Najeriya.

Asali: Facebook
NDLEA ta wallafa a shafinta na Facebook cewa an cafke Obehi a filin jirgin sama na kasa da ke Fatakwal, a ranar Lahadi yayin da take shirin shiga jirgin Qatar Airline zuwa Iran ta Doha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda NDLEA ta kama mai safarar kwayoyi
Aminiya ta wallafa cewa daraktan hulda da jama’a na NDLEA a Abuja, Femi Babafemi, ya ce jami’an NDLEA sun gano cewa matar ta ɓoye kullin kwayoyi guda uku a al'aurarta.
Haka kuma, ta ɓoye wasu manyan kwayoyi guda biyu a cikin wani sashe na jakarta, sannan ta hadiye kwayoyi guda 67.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Sakamakon haka ne aka sa mata ido, domin ta fitar da kwayoyin da ta hadiye. Bayan kwanaki da yawa, sai ta kasar da kwayoyi 67 da ta hadiye a cikinta. Ta bayyana cewa an shirya za ta hadiye kwayoyi 70 ne, amma bayan ta hadiye guda 67, ta kasa ci gaba da hadiyewa sai ta saka sauran guda uku cikin al'aurarta.”
Hukumar NDLEA ta yi kame a Legas
Jami’an NDLEA a filin jirgin sama na Murtala Mohammed Ikeja, Legas sun cafke wani ɗan ƙasar Birtaniya mai shekaru 22 mai suna Campell Kaizra Kofi Johannes Slifer da safarar kwayoyi.
Campell ya iso Najeriya daga Thailand ta jirgin Qatar Airways dauke da jakunkuna biyu da ke ɗauke da kwayoyi 35 na Loud, wata irin ƙwayar hodar iblis wacce nauyinta ya kai kilo 37.60.
Matashin, wanda ya ce an taɓa yanke masa hukunci sau biyu a Birtaniya saboda safarar kwayoyi da fashi da makami, an ba shi kwayoyin daga Landan ya ya kawo Najeriya.
NDLEA ta gano gonar wiwi a Kano
A wani labarin, kun ji cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) reshen Kano ta kai samame wata gona da ake zargin ana noman tabar wiwi a ciki.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da hukumar ke gano irin wannan gona ba, sai dai a wannan karon an kama wani dattijo da ake zargin shi ne mai gonar da aka yi basaja a ciki.
NDLEA ta bakin kakakinta a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ta ce jami’anta sun cafke wani dattijo mai suna Malam Sabo bayan gano gonar da ke cike da bishiyoyin tabar wiwi.
Asali: Legit.ng