Yadda Dangote Ya Sake Rage Kudin Litar Man Fetur a Najeriya

Yadda Dangote Ya Sake Rage Kudin Litar Man Fetur a Najeriya

  • Matatar Dangote ta rage farashin fetur daga N835 zuwa N825 domin ƙarfafa gasa da jan hankalin abokan ciniki
  • Hakan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan ganawar Dangote da sabon shugaban NNPCL, Bayo Ojulari a birnin tarayya, Abuja
  • Dangote ya bayyana cewa babu gasa tsakaninsa da NNPCL, yana mai cewa lokaci ne na haɗin gwiwa don kawo cigaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Matatar Dangote ta sanar da rage farashin fetur daga N835 zuwa N825 a wani yunƙuri na ƙara janyo hankalin abokan ciniki da kuma ƙarfafa matsayinta.

Rahotanni sun nuna cewa rage farashi ya zo ne makonni kaɗan bayan rage kudin litar mai daga N865 zuwa N835.

Dangote
Dangote ya rage kudin litar man fetur. Hoto: Dangote Industries|Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton Vanguard ya nuna cewa sauyin farashin wani mataki ne na matatar na saukakawa abokan cinikinta da kuma nuna cewa tana da ƙarfi a kasuwar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ya kai ziyarar ban girma ga sabon shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Bashir Bayo Ojulari.

Dangote ya rage farashin man fetur

Business Day ta rahoto cewa tun a watan da ta gabata ne matatar Dangote ta rage farashin litar mai daga N865 zuwa N835, sannan yanzu ta sake rage farashin zuwa N825.

Rahotanni sun nuna cewa matakin zai iya tilasta sauran masu sayar da fetur su bi wannan hanyar sauke farashi.

A makon da ya wuce, Aliko Dangote ya gana da shugaban kamfanin NNPCL, Bashir Bayo Ojulari a Abuja

Ya bayyana cewa matatar Dangote da NNPCL za su ci gaba da aiki tare domin tabbatar da isasshen makamashi ga ‘yan Najeriya.

NNPCL
Dangote ya gana da shugabannin NNPCL. Hoto: Dangote Industries.
Asali: Getty Images

Dangote ya kuma yaba da ƙwarewar sabon shugabancin NNPCL, yana mai bayyana cewa ya na da tabbacin za su iya fuskantar kalubalen da ke gabansu tare da samun nasara.

NNPCL ya yarda da haɗin kai da Dangote

A nasa jawabin, sabon shugaban NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana cewa zai tabbatar da cewa alaƙar dake tsakanin kamfaninsu da Dangote ta ci gaba da zama mai amfani ga ƙasar nan.

Ojulari ya jaddada cewa ma’aikatan NNPCL na da ƙwarewa da himma wajen tabbatar da samar da daraja ga Najeriya.

Amfanin rage farashin mai ga ‘yan Najeriya

Rage farashin fetur daga matatar Dangote zai iya rage nauyin da ke kan ‘yan Najeriya, musamman a lokaci da ake fama da tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin fetur.

Haka nan, ƙarfafa gasa tsakanin matatar Dangote da sauran masu sayar da fetur na iya sa farashi ya sauka.

NNPCL zai cigaba da hako mai a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kamfanin NNPCL ya ce za a cigaba da aikin hako man fetur a yankin Arewacin Najeriya.

A wata hira da aka yi, Bayo Ojulari ya ce aikin hako man fetur a Arewa zai bunkasa tattalin yankin tare da farfado da masana'antu.

Tun a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari aka fara hako man fetur a Kolamani dake tsakanin Gombe da Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng