NLC: An Yi wa Dangote Barazana kan Dauko Ma'aikata daga Arewa zuwa Legas

NLC: An Yi wa Dangote Barazana kan Dauko Ma'aikata daga Arewa zuwa Legas

  • Ƙungiyar kwadago ta NLC reshen Legas ta ce an kawo matasa 89 daga Katsina ba bisa ka’ida ba domin aiki a matatar Dangote da ke Ibeju-Lekki
  • 'Yan kwadago sun zargi matatar da karya dokokin kwadago tare da barazana ga tsaron yankin da mazauna suka damu da shigowar matasan
  • Ta bukaci Gwamnan Jihar Legas da Ma’aikatar Kwadago ta Tarayya su sa baki, tare da yin barazanar yajin aiki idan ba a janye matasan ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Ƙungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Legas ta yi barazanar yajin aiki bisa zargin da ake yi wa matatar Dangote kan shigo da matasa 89 daga jihar Katsina ba tare da bin doka ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an hango matasan cikin wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta suna sauka daga mota a gaban wani kamfani kusa da matatar Dangote.

Dangote
'Yan kwadago sun ce Dangote ya karya dokar daukar ma'aikata. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa rundunar ‘yan sandan Legas ta ce matasan sun samu aikin ne bisa doka, amma NLC ta nace cewa shigowar su barazana ce ga tsaro da kuma karya doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta zargi Dangote da karya doka

Shugabar NLC a jihar Legas, Funmi Sessi, ta bayyana cewa abin da matatar Dangote ta yi ya sabawa dokokin aikin yi da kuma ƙa’idojin da aka tsara.

Funmi Sessi ta ce:

“Dokar kwadago ta fayyace cewa akalla kashi 70 cikin 100 na ma’aikata marasa ƙwarewa dole ne su fito daga yankin da aikin ke gudana.
"Amma sai ga shi Dangote ya kawo matasa daga Katsina, alhali akwai matasa marasa aikin yi a Legas,”

Ta ce babu wata ƙwarewa da waɗannan matasa daga Arewa ke da ita da matasan yankin Legas ba su da ita.

NLC NG
'Yan kwadago sun gargadi Dangote kan daukar matasa aiki daga Katsina. Hoto: NLC HQ
Asali: Facebook

Shugabar ta kara da cewa abin da Dangote ya aikata ba za a amince da shi ba domin yana tauye ‘yancin mazauna yankin.

An nemi gwamnati ta sa baki cikin gaggawa

Kwamared Sessi ta ce NLC ba za ta zuba ido Dangote na tauye ma’aikata ba tare da ɗaukar mataki ba.

Ta bukaci Gwamna Babajide Sanwo-Olu da Ma’aikatar Kwadago ta Tarayya su sa baki cikin gaggawa.

Shuagabar ta ce:

“Wannan ba shi ne karon farko da Dangote ke irin wannan ba.
"Yana yawan shigo da ‘yan Indiya da sauran baki domin yin aikin da ‘yan Najeriya za su iya.”

Ta ƙara da cewa NLC na shirin ɗaukar matakin ƙasa baki ɗaya idan Dangote ya gaza maida matasan Katsina zuwa wani kamfaninsa a Arewacin Najeriya.

Dangote zai ba matasan Najeriya horo

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin Dangote ya bude kofa domin daukar matasan Najeriya aikin wucin gadi.

Kamfanin Dangote ya ce za a dauki matasan ne domin a ba su horo na musamman wajen aiki da shi na wani lokaci.

An bayyana cewa dole duk wani matashin Najeriya da zai nemi aikin ya kasance ya kammala karatun a jami'a da sauransu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng