Gobara Ta Lalata Kayayyaki Masu Yawa a Fadar Sarkin Daura

Gobara Ta Lalata Kayayyaki Masu Yawa a Fadar Sarkin Daura

  • Mummunar gobara ta janyo asarar kayayyakin miliyoyin naira a fadar sarkin Daura da ke a jihar Katsina
  • Gobarar dai ta tashi ne a wani sashi na gidan inda Yariman sarkin Daura yake zaune tare da iyalansa a fadar
  • Ba a samu asarar rai ba a dalilin gobarar wacce ake tunanin ta tashi ne a dalilin tangarda da aka samu da wutar lantarki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Daura, Jihar Katsina - An yi asarar kayayyakin miliyoyin naira a gobarar da ta tashi a fadar mai martaba sarkin Daura.

Jaridar Daily Trust ta yi rahoto cewa gobarar wacce ta fara da wajen misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Litinin, ta kwashe lokaci mai tsawo tana ci inda ta lalata kusan komai na wani sashi a fadar.

Gobara ta lakume kaya masu yawa a fadar Sarkin Daura
Wani bangare inda gobarar ta lalata Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Sashin da gobarar dai ta laƙume na ɗan Sarkin ne, mai riƙe da sarautar Danburam na Daura. Yariman masarautar, Alhaji Muhammadu Daha Umar Farouq Umar, shi ne dagacin Baure.

Kara karanta wannan

Jimami Yayin da Dan Takarar Majalisar Tarayya a Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Ba a samu asarar rai ba a mummunar gobarar

Majiyoyi sun bayyana cewa ba a yi asarar rayuka ba domin matarsa wacce ɗiya ce a wajen marigayi Sarki Muhammad Bashir, ta yi tafiya lokacin da gobarar ta auku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Babu abinda aka fitar daga sashin da gobarar ta lalata, inda Allah ya taƙaita babu kowa a cikin gidan." A cewar majiyar.
"Abubuwa masu daraja sosai sun lalace ciki har da muhimman takardu a cikin gidan."

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin masarautar, Sarkin Labaru Usman Yaro, ya bayyana cewa duk da dai ba a tabbatar da maƙasudin tashin gobarar ba (a lokacin haɗa wannan rahoton), gobarar ta yiwu ta tashi ne a dalilin wutar lantarki saboda gidan a kulle yake lokacin da ta tashi.

Ya nuna godiyasa ga jami'an ƴan kwana-kwana da al'ummar Daura waɗanda suka taimaka wajen kashe gobarar.

Kara karanta wannan

Sabuwar Shekarar Musulunci: Gwamnan PDP Ya Bayyana Ranar Laraba a Matsayin Ranar Hutu a Jiharsa

Gobarar ta yi ɓarna sosai

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin garin Daura mai suna Abubakar Abdulrahman, wanda ya bayyana cewa gobarar ta yi gagarumar ɓarna sosai a gidan.

Ya bayyana cewa gobarar ta kama ɓangaren da uwargidan Yariman Sarkin ta ke zaune ne na cikin gidan, inda ya ce babu wani abu mai amfani da ya tsira a dalilin gobarar.

Abubakar ya ce gobarar ta ɗauke dogon lokaci kafin daga bisani aka samu aka kashe ta. Ya ce ta fara ne tun kusan misalin ƙarfe 4:00 na yamma inda ta kai har bayan ƙarfe 8:00 na dare.

Ya bayyana cewa har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

Gobara Ta Kona Gidan Shugaban Kungiyar Ƙwadago

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa wata mummunar gobara ta tashi a gidan shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Har Cikin Fada, Sun Halaka Babban Sarki a Najeriya

Mummunar gobarar ta tashi ne a gidansa da ke a birnin Legas inda ta laƙume komai dake a cikin gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel