Gwamnan Jihar Filato Ya Nada Sabbin Manyan Sakatarori Guda 5

Gwamnan Jihar Filato Ya Nada Sabbin Manyan Sakatarori Guda 5

  • Gwamnan jihar Filato ya naɗa sabbin manyan Sakatarori 5 makonni biyu bayan ya kori waɗanda tsohon gwamna Lalong ya naɗa
  • Caleb Mutfuwang, ya ce zai rantsar da sabbin mutanen da ya naɗa ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, 2023
  • Wannan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Gyang Bere, ya fitar ranar Talata

Plateau - Gwamnan jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, Caleb Mutfwang, ya naɗa sabbin Sakatarori guda 5 ranar Talata, 20 ga watan Yuni, 2023.

Punch ta ce gwamnan ya yi wannan nadi ne mako biyu bayan ya kori baki ɗaya manyan Sakatarorin da tsohon gwamna, Simon Lalong, ya naɗa a zamanin mulkinsa.

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang.
Gwamnan Jihar Filato Ya Nada Sabbin Manyan Sakatarori Guda 5 Hoto: Caleb Mutfwang/facebook
Asali: Facebook

Sabbin manyan sakatarorin da gwamna Mutfwang ya amince da naɗinsu na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren watsa labaransa, Gyang Bere, ya fitar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Naɗa Kwamishinoni 19, Ya Tura Sunayensu Ga Majalisar Dokokin Kano

Wani sashin sanarwan ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A yunkurinsa na garambawul da farfaɗo da ɓangaren ma'aikata, mai girma gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Manasseh Mutfwang, ya amince da naɗa sabbin manyan Sakatarori."
"Waɗanda mai girma gwamna ya naɗa zasu cike gurbin da ake da su a sashin ma'aikatan jihar Filato."

Jerin sunayen sabbin manyan sakatarorin

Sanarwan ta kuma jero sunayen mutanen da Allah ya ci da, waɗanda gwamnan ya naɗa a matsayin, ga su kamar haka:

1. Helen H. Chundusu

2. Roseline Kefas Dakwar

3. Barista Joel Zhidih Tahvan

4. Nanman Jonah Kparbong

5. Aishatu Ibrahim Saleh.

Yaushe zasu kama aiki a sabon muƙaman da aka naɗa su?

Bugu da ƙari, sanarwan ta yi bayanin cewa gwamna zai shaida rantsuwar kama aikin sabbin Sakatarorin ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, 2023, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan Arewa Ya Yi Shiga Mai Ban Mamaki, Ya Kai Ziyarar Bazata Wani Asibiti a Keke Napep

"Mai girma gwamna zai rantsar da sabbin manyan sakatarorin ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, 2023 a ɗakin taron Victoria Gowon Hall da misalin karfe 11:00 na safe."
"Muna fatan duk wanda aka gayyata ya shaida rantsuwar zai zauna a wurin da aka tanadar masa tun da karfe 10:30 na safe dan Allah," inji sanarwan.

Shugabannin PDP 7 da Suka Yi Murabus, Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

A wani rahoton na daban kuma Tsoffin shugabannin PDP 7 a jihar Imo sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Mambobi 7 na kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP reshen jihar Imo (SWC), waɗanda suka fice daga jam'iyyar a 'yan kwanakin da suka wuce, sun shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel