Shugaba Tinubu Ya Haɗu da Peter Obi a Bikin Naɗin Fafaroma, An Ji Abin da Suka Tattauna

Shugaba Tinubu Ya Haɗu da Peter Obi a Bikin Naɗin Fafaroma, An Ji Abin da Suka Tattauna

  • Bola Ahmed Tinubu ya haɗu da tsohon ɗan takarar LP, Peter Obi da Dr. Kayode Fayemi a wurin bikin naɗa sabon Fafaroma, Leo XIV
  • Rahotanni sun nuna Fayemi da Mista Obi sun je har wurin da Shugaban kasa Bola Tinubu ke zaune a taron, kuma sun tattauna da juna
  • Fayemi, tsohon gwamnan jihar Ekiti da Obi, tsohon gwamnan Anambra sun halarci naɗin Fafaroma ne a karan kansu, ba daga cikin tawagar shugaban kasa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rome, Italy- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya haɗu da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi a wurin bikin naɗin sabon Fafaroma a ƙasar Italiya.

Bola Tinubu, Peter Obi da tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma tsohon minista a zangon mulkin Buhari na farko, Kayode Fayemi sun haɗu a birnin Rome ranar Lahadi.

Obi, Fayemi da Tinubu.
Shugaban Kasa Tinubu ya haɗu da Peter Obi da Fayemi a wurin rantsar da fafaroma Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa manyan jiga-jigan sun ɗan tattauna da gaisawa a tsakaninsu yayin da suka halarci bikin naɗin sabon Fafaroma, Leo XIV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Leo CIV ya zama sabon Fafaroma ne bayan mutuwar Fafaroma Francis a ranar Litinin da ake bikin Easter.

Shugaba Tinubu ya haɗu da Peter Obi?

Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, shi ne ɗan takarar da ya gwabza a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a inuwar LP amma ya sha kashi a hannun Shugaba Bola Tinubu.

A cewar rahotanni, Fayemi ya hango Shugaba Tinubu daga wurin da yake zaune tare da wasu shugabanni a wurin naɗin sabon jagoran cocin Katolika na duniya.

Bayan hango Shugaba Tinubu, Fayemi ya jingine siyasa wuri ɗaya, ya roki Mista Obi da su je su gaishe da mai girma shugaban kasa.

Yayin da suka isa wurin Bola Tinubu, rahotanni sun nuna cewa Fayemi ya fara magana, inda aka ji yana yi wa shugaban ƙasar barka da zuwa bikin naɗin Fafaroma.

Me Tinubu ya faɗawa Peter Obi da Fayemi?

Fayemi ya fara da cewa:

"Mai girma Shugaba, barka da zuwa cocinmu, mun gode da ka girmama Fafaroma kuma ka halarci wannan taro da kanka.”

Shugaba Tinubu ya amsa da cewa:

“Ai ni ya kamata na ce maku barkan ku da zuwa nan domin ni ne jagoran tawagar Najeriya a nan.”
Fayemi, Obi da Shugaba Tinubu.
Yadda tattaunawa ta kaya tsakanin Shugaba Tinubu, Kayode Fayemi da Peter Obi Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Wannan magana da ake ganin shugaban kasa ya yi ta cikin barkwanci ta ba Peter Obi dariya, sannan ya amsa da cewa:

"Maganarka haka take, gaskiya. Mu 'yan tawagarka ne.”

Mista Obi da Dr. Kayode Fayemi dukan su mambobi ne na cocin Katolika kuma suna da matsayin fada wanda fafaroma ya ba su, kamar yadda Punch ta rahoto.

Tinubu ya halarci bikin naɗin sabon Fafaroma

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci tawagar ƴan Najeriya zuwa wurin naɗin sabon Fafaroma na cocin Katolika, Leo XIV.

Shugaba Bola Tinubu ya tafi Rome tare da wasu muhimman mutane a gwamnatinsa, ciki har da Ƙaramar Ministan Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu.

Ana sa ran shugaban kasa Bola Tinubu zai dawo gida Najeriya a ranar Talata, 20 ga Mayu, bayan kammala taron da ake ganin zai hada shugabanni daga fadin duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262