EFCC Ta Gano Yadda Kudin Kasashen Waje ke Sauka kamar Ruwan Sama a Asusun Malami a Najeriya
- Hukumar EFCC ta gano yadda ake turo Dalolin Amurka da kudin Ingila zuwa asusun Fasto Jerry Eze daga kasashe daban-daban
- Shugaban EFCC na kasa, Ola Olukoyede ya ce ya gudanar da bincike kan limamin cocin na tsaw/on watanni shida kan zargin halasta kudin haram
- Sai dai a cewarsa, daga baya ya gano cewa Fasto Eze mutumin kirki ne bayan ya gana da shi a hedkwatar EFCC da ke Abuja
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa ya shafe watanni shida yana binciken Fasto Jerry Eze kan zargin halasta kudin haram.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a wani taro da gidauniyar Jerry Eze ta shirya na rabon tallafin kasuwanci a babban birnin tarayya Abuja yau Laraba.

Source: Facebook
A rahoton Channles tv, ya bayyana cewa hukumar ta lura da wani asusun banki na kudaden waje, inda Dalar Amurka da fam din Ingila ke "shiga kamar ruwan sama" daga kasashe daban-daban.
Yadda EFCC ta binciki Fasto Jerry Eze
Shugaban EFCC ya ce:
"Ban taba son fadar hakan ba, amma na ji cewa wannan ita ce kadan daga cikin gudunmawar da zan bayar. Na gudanar da bincike a kan wannan mutumin (Fasto Jerry Eze) na tsawon watanni shida kan zargin halatta kudaden haram.
"A baya mun samu rahoton wani asusun banki da Dalar Amurka da Fam din Ingila suka rika kwarara kamar ruwan sama daga kasashen Colombia, Amurka, Sri Lanka, har ma da Togo.
"Sai na ce, waye wannan mutumin? Tabbas, ina jin sunansa, kuma na taba ganin fuskarsa amma ban damu da abin da yake yi ba tun da fasto ne."
"Aka ce mini ai Fasto Jerry Eze ne na cocin Streams of Joy, take na bayar da umarnin a gudanar da bincike a kansa; mun binciko bayanan banki, kuma tabbas mun ga kudade na shigowa," in ji shi.
Me binciken hukumar EFCC ya gano?
Olukoyede ya kara da cewa jami’in EFCC ya kawo masa rahoton farko kan binciken da aka yi, inda ya bukaci a gayyato Fasto Jerry Eze domin ganawa da masa tambayoyi

Kara karanta wannan
Emefiele: An ji yadda aka yi amfani da sa hannun Buhari aka cire makudan kudi a bankin CBN
Ya ce da farko bai gane shi ba lokacin da ya zo ofishinsa domin ya yi mamakin yadda ya gan shi cikin kaya marasa tsada, har ya kusa ce masa ya je ya kira fastonsa.
Bayan kammala bincike, Olukoyede ya ce faston ya bayyana masa yadda kudaden ke shigowa da kuma yadda yake amfani da su wajen taimakon jama’a, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Instagram
Olukoyede ya yabawa Fasto Jerry Eze bisa yadda yake tafiyar da harkokinsa, inda ya la kara da cewa EFCC na da alhakin hana laifuffuka tare da goyon bayan mutanen kirki masu gaskiya.
EFCC ta ayyana neman shugabar CBM
Awani rahoton, kun ji cewa EFCC ta ayyana neman Halimat Adenike Tejuosho, shugabar matan ƙungiyar City Boy Movement ruwa a jallo kan zargin damfara.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa ana neman Tejuosho ne don amsa tambayoyi game da zargin zamba da karɓar kuɗaɗe ta hanyar yaudara.
Hukumar EFCC ta yi kira ga duk wanda yake da bayanan da za su kai ga kamo Halimat Adenike Tejuosho da ya tuntuɓi ofisoshinsu da ke faɗin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng
