Bidiyon Tsiraicin Sisi Mai Maganin Mata Ya Bazu a Intanet, Ta Fita Ta Yi Magana

Bidiyon Tsiraicin Sisi Mai Maganin Mata Ya Bazu a Intanet, Ta Fita Ta Yi Magana

  • Fitacciyar mai amfani da kafar sada zumunta tana sayar da magani, Sisi Alagbo ta tuba kan fitar bidiyon tsiraicinta da ya yadu sosai a intanet
  • Rahoto ya nuna cewa Sisi Alagbo ta nuna cewa ta shiga halin damuwa kan fitar bidiyo, lamarin da ya kai ga hana ta cin abinci saboda takaici
  • Ta bayyana cewa za ta nemi gafarar Ubangiji kan lamarin, tare da kira ga jama'a da suka kaucewa tattauna batun a tsakaninsu a kafafen sadarwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ana cigaba da magana kan bidiyon tsiraicin fitacciyar mai amfani da kafar sada zumunta tana sayar da magungunan gargajiya, Eniola Fagbemi, wacce aka fi sani da Sisi Alagbo.

Biyo bayan bazuwar lamarin, Sisi Alagbo ta roƙi gafara kan bidiyon lalata na mutum uku da ya haɗa da ita, mijinta (Adesola Hakeem) da wata mata.

Kara karanta wannan

Tsaro: Kasar Jamus ta shigo Najeriya, ta shiga kauyukan da aka kai hare hare

Sisi Alagbo da ake magana a kanta
Sisi Alagbo da bidoyonta ya bazu a intanet. Hoto: Eniola Sisi Alagbo
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa Sisi Alagbo ta yi maganar neman afuwa game da bidiyon ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Bidiyon tsiraicin Sisi Alagbo da ya fita

Bidiyon tsiraicin, wanda ya bazu a ranar Litinin amma wakilinmu bai gan shi ba, ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin masu amfani da kafar sada zumunta.

Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama suka nuna kyama ga yadda aka tsara lamarin, yayin da wasu ke tambayar dalilin wannan dabi’a tasu.

Halin da Sisi Alagbo ta shiga

Fagbemi ta bayyana irin halin da take ciki, inda ta ce ta shafe kwanaki ba ta iya barci ba, har ma magungunan barci sun daina yi mata aiki tun bayan da bidiyon ya bazu a intanet.

A ranar Laraba, ta rubuta cewa:

“Na amince da kuskurena, kuma ina roƙon gafara kan bidiyon da ke yawo a intanet. Ina matuƙar baƙin ciki ga duk wanda na ɓata wa rai.

Kara karanta wannan

OPEC+: UAE ta dauki mataki 1 da ya girgiza Saudiyya da kasuwar mai ta duniya

“Wannan lokaci ne mai wahala a gare ni, ina roƙon gafarar Allah da kuma ta masoyana.
"Don Allah mu wuce wannan al’amari, domin wannan kafar ce nake samun ɗan tallafi don ciyar da kaina gaba. Don Allah kada ku hukunta ni ko ku tsangwame ni, domin ina cikin wani hali mai tsanani.
“Ba na iya cin abinci ko barci tsawon kwanaki, har magungunan barci ma ba sa yi min aiki. Ina matuƙar baƙin ciki, ku yafe min don Allah. Ba na son cutar da kaina.”
Sisi Alagbo yayin tallata magani
Sisi Alagbo mai maganin gargajiya. Hoto: Eniola Sisi Alagbo.
Source: Instagram

Punch ta wallafa cewa Fagbemi ta shahara a intanet ne saboda tallata kasuwancin kakarta zuwa sassa daban-daban na duniya, ciki har da China da Qatar.

Bidiyon tsiraicin Safara'u ya fita

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohuwar jarumar Kannywood, Safiyya Yusuf da aka fi sani da Safara'u ta yi magana kan bidiyonta da ya fita.

Yayin da take bayani ga jama'a, ta bayyana cewa ta yi bidiyon tsiraicin ne domin nishadantar da kanta ba wai da wata manufa ta dabam ba.

Safara'u ta kara da cewa wani ne ya yi kutse a wayarta ya tura bidiyon ba kamar yadda wasu ikirarin cewa ita da kanta ta turawa saurayinta ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng