"Ta Mutu da Wuri," Gwamna Ya Faɗi Abin da ke Ƙona Masa Rai game da Rasuwar Mahaifiyarsa

"Ta Mutu da Wuri," Gwamna Ya Faɗi Abin da ke Ƙona Masa Rai game da Rasuwar Mahaifiyarsa

  • Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya tuna da kyawawan halayen mahaifiyarsa wacce ta rasu tun a 2012, yana mai cewa ta tafi da wuri
  • Mai girma gwamnan ya ce duk halayen kirki da ake gani tattare su, daga wurinta suka koya, ya ce ta kasance mace mai tsoron Allah da kamun kai
  • Diri ya faɗi haka ne a wurin bikin tunawa da mahaifiyarsa, marigayiya Madan Rose Diri karo na 12 a garin Ayamasa a jihar Bayelsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana mahaifiyarsa, Madam Rose Diri a matsayin mace mai kamun kai, wacce ta ba ƴaƴanta tarbiyya mai kyau.

Gwamna Diri ya tuna kyawawan halayen mahaifiyarsa ne a wurin bikin tunawa da ita karo na 12 da aka gudanar a garin Ayamasa, ƙaramar hukumar Ekeremor.

Gwamna Douye Diri.
Gwamna Douye Diri ya tuna da kyakkyawar tarbiyyar da marigayiya mahaifiyarsa ta ba su Hoto: Douye Diri
Asali: Twitter

Diri ya ce mahaifiyarsu ta koya musu darussa na ƙauna, zaman lafiya da daraja addini, waɗanda kowa ke gani a tattare da su a yanzu, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai gwamnan ya nuna takaicinsa bisa rashin Madam Rose, yana mai cewa ta mutu da wuri tun kan ta girbi tarbiyyar da ta shuka a jikin ƴaƴanta ba.

Madam Rose Diri ta rasu a ranar bikin tunawa da ranar haihuwarta, 15 ga Mayu, 2013 tana da shekaru 74.

Gwamna Diri ya sake tunawa da mahaifiyarsa

Da yake jawabi, gwamnan ya ce:

“Ina kallon mahaifiyata a matsayin mace tagari kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana a Misalai 31. Mahaifiyata ta rayu cikin tsoron Allah kuma ta tarbiyantar da mu bisa wannan hanya.
"Duk wata dabi’a ta kirki da muke nuna wa a yau, ita ta ɗora mu a kai. Ta buɗe ƙofa ga kowa, dangi, abokai, baƙi, kuma ta ɗauki dukan yaran mahaifina kamar nata ne. Wannan ya sanya muke da haɗin kai har yanzu.”

“Abin da nake matuƙar bakin, nadama da takaici shi ne ta mutu da wuri tun ba ta ci moriyar 'ya'yan da ta bai wa tarbiyya ba."

Gwamna Diri ya so canza al'adar Ijaw

Gwamna Diri ya kuma bayyana yadda ra’ayinsa ya sauya kan al’adar Ijaw da ke buƙatar a binne mace a garin mahaifanta maimakon wurin mijinta.

Ya ce kafin ya zama gwamna, bai fahimci hikimar hakan ba, amma yanzu ya fahimta.

Gwamna Douye Diri.
Gwamna Diri ya ce ya so canza al'adar Ijaw kafin ya fahimci hikimar da ke ciki Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook
“Da farko, ban goyi bayan wannan al’ada ba. Na ce da zan samu dama sai na sauya ta. Amma yanzu na fahimci cewa wannan al’ada ce ta haɗin kai da tunawa da zuriyya.”
“Saboda wannan al’ada, na fara zumunci da dangin mahaifiyata kuma hakan ya ƙara faɗaɗa haɗin kanmu. Ban yi nadamar cewa sai mun zo nan a Ayamasa domin tunawa da ita ba.”

- Douye Diri.

Gwamna Diri ya rufe jawabin nasa da godiya ga jama’ar Ayamasa bisa irin karɓar da suke yi masa da iyalinsa, yana mai cewa mahaifiyarsa za ta ci gaba da zama abin koyi da karramawa.

Gwamna Diri ya tuna yadda ya nemi mulki

A baya, kun ji cewa Gwamna Douye Diri ya bayyana yadda ya bi bokaye domin neman nasara a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.

Sanata Diri ya bayyana yadda babban mutum ya bukace shi ya yi wata yanka a Abuja, amma ya ki saboda yakininsa da Ubangiji.

Har ila yau, Diri ya bayyana yadda ya biya wasu 'yan tsibbu a Kenya $10,000 kimanin N5m domin kokarin taimaka masa ya zama gwamna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262