Hisbah Ta Kano Ta Kwace Kwalaben Giya 8,600, Ta Kama 15 Kan Karuwanci

Hisbah Ta Kano Ta Kwace Kwalaben Giya 8,600, Ta Kama 15 Kan Karuwanci

  • Jami'an Hukumar Hisbah a jihar Kano sun yi nasarar cafke wata mota makare da kwalaben giya a kalla 8,600 tare da direban motan
  • An kama motar ne a kusa da kauyen Kwanan Dangora bayan da 'yan Hisba suka rika bibiyar motar tun daga jihar Kaduna
  • 'Yan Hisban sun kuma kama wasu 'yan mata akalla 15 a wurare daban-daban a jihar ta Kano da ake zargi da yin karuwanci cikinsu har da wadanda aka kama a baya

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kwace kwalaben giya akalla 8,600 da aka shake mota da su daga jihar Kaduna.

Jami'in hukumar mai kula da sashin shan abubuwan maye, Idris Ibrahim, ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Asabar.

Hisbah ta kama kwalaben giya 8,600 a Kano
Hisbah ta Kano ta kama kwalaben gida da karuwa. Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Ibrahim ya ce an kwace abubuwan barasan a ranar Alhamis da ta gabata a Kwanar Dangora kan babban hanyar Kano zuwa Kaduna.

Ya kara da cewa jami'an hukumar sun rika bibiyar motar daga Kaduna har zuwa lokacin da ta shigo yankin jihar Kano.

Ibrahim ya ce:

"Mun tsayar da motar a kwanar Dangora kuma direban ya yi kokarin tserewa amma jami'anmu suka kama shi.
"Ka san cewa haramun ne sha da siyar da giya a jihar Kano. Don haka za mu kai direban kotu bayan daukan bayaninsa."

Ya kara da cewa tawagar Hisbah masu yaki da barasa suna jiran umurni na gaba daga mahukunta a hukumar.

Yan Hisbah sun kama mata karuwai 15 a Kano

A bangare guda, hukumar ta kama matasa mata 15 a wurare daban-daban a birnin Kano.

An gano cewa an kama matan da ake zargi da karuwancin ne a Hotoro Tishama, Bakin River Verd Sabon Gari, Hadejia Road da Old Zoo Road motor park.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Mataimakin kwamandan Hisbah, Dr. Mujahid Aminuddeen, ya tabbatar da kamen ya ce wasu cikin wadanda aka kama din an taba kama su a baya an kai su kotu amma ba su dena haramtaccen aikin ba.

"Abin takaici ne mata su baro jihohinsu da kasashensu su zo Kano don yin karuwanci da wasu halaye marasa kyau.
"Suna gararamba a titi suna aikata abubuwa daban-daban. Muna kira ga mutane su rika kawo mana rahoton irinsu don mu tsaftace jihar.
"Sai dai, wasu cikin matan na bukata addu'a don idan ka yi magana da su, za ka fahimci wahala ce ta jefa su cikin lamarin," in ji Aminuddeen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel