Aikin Allah: Hisbah Ta Dauki Mataki Bayan Kama Kwalaben Giya a Katsina

Aikin Allah: Hisbah Ta Dauki Mataki Bayan Kama Kwalaben Giya a Katsina

  • Hukumar Hisbah a jihar Katsina tana ci gaba da aikin tsaftace jihar daga dukkan badala da ayyukan assha
  • Jami’an hukumar sun yi nasarar kamawa tare da lalata kwalaben giya masu yawa a yankin Kankara da ke jihar
  • Kwamandan Hisbah a jihar, Dr Aminu Usman, ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tarbiyya da yakar miyagun halayya a jihar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Hukumar Hisbah ta jihar Katsina, ta ce jami'anta sun lalata kwalaben giya iri-iri guda 850 a karamar hukumar Kankara da ke jihar.

Kwamandan Hisbah a jihar, Dr Aminu Usman, (Abu-Ammar) ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Katsina, a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Yan hisbah sun fasa kwalaben giya
Aikin Allah: Hisbah ta dauki mataki bayan kama kwalaben giya a Katsina Hoto: Punch
Asali: UGC

A cewarsa, ya jagoranci kona kwalaben giyan a ranar Lahadi a Kankara tare da wasu jami'an gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma jadadda jajircewar gwamnatin jihar wajen yaki da munanan dabi'u a jihar.

Yadda jami'an Hisbah suka kama motar giya a Katsina

Mallam Usman ya kuma yi bayanin cewa an kama wata mota dauke da giya wacce ta doshi cikin gari, an kuma kwace wasu daga inda ake siyar da su a cikin karamar hukumar.

A cewarsa, dokar kafa hukumar ta bai wa Hisbah damar shiga lungu da sako na jihar domin neman wuraren da ake aikata barna, rahoton Leadership.

Kwamandan ya kuma roki jama'ar jihar da su dunga fallasa gidaje ko wuraren da ake aikata irin wadannan badalar a garuruwansu.

Ya yi kira ga jama'a da su dunga goyon bayan hukumar wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a kodayaushe domin tsarkake jihar ta yadda kowa zai ji dadin zama a cikinta.

Kara karanta wannan

Bayin Allah sama da 100 sun mutu yayin da bama-bamai suka tashi a wurin taro kusa da Masallaci

Hisbah ta dau mataki kan mabaratan Katsina

A gefe guda, mun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta jaddada kudirinta na daukar mataki kan yawaitar barace-barace a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.

Dr Aminu Usman (Abu-Ammar), babban kwamandan hukumar Hisbah a Katsina ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Asabar.

A cewarsa, gwamnatin jihar na yin duk mai yiwuwa don tsaftace jihar daga duk wani nau’in lalata da barnar da ka iya biyo baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel