Dusashewar karfin mazakuta: 'Yan sanda sun fara binciken wani mutum da laifin 'shafi mulera'

Dusashewar karfin mazakuta: 'Yan sanda sun fara binciken wani mutum da laifin 'shafi mulera'

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Enugu sun fara binciken korafin da wani mutum, Mista Sunday, ya shigar a gabanta bisa dusashewar karfin mazakutarsa bayan ya gaisa da wani gurgu mai suna Anayo.

SP Ebere Amaraizu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Enugu, ya tabbatar da faruwar hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Lahadi.

Amaraizu ya ce lamarin ya faru ne ranar 13 ga watan Satumba a yankin kwanar Obiagu da ke unguwar Ogui a cikin birnin Enugu.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce wanda ake zargi da aikata laifin 'shafi mulera' yana da nakasa (bukata ta musamman)

"Hedikwatar 'yan sanda na gudanar da bincike ta hannun ofishinta da ke unguwar Ogui domin warware rudanin da ke tattare da korafin da wani mutum ya shigar a kan dusashewar karfin mazakutarsa jim kadan bayan ya gaisa da wani mutum a Enugu.

DUBA WANNAN: Abin da kisan mabiyan mu zai haifar wa gwamnatin Buhari - Jigo a Shi'a

"Mutumin mai suna Sunday ya ankarar da jama'a abin da ya faru kuma ya nuna mutumin da yake zargi da daukewar karfin mazakutarsa bayan sun gaisa.

"Yana zargin wani mai suna Anayo da dusashewar karfin mazakutarsa, lamarin da yasa jama'a suka lakada masa shegen duka kafin daga bisani jami'an 'yan sanda daga ofishin Ogui su kwace shi da kyar," a cewarsa.

Amaraizu ya ce rundunar 'yan sanda na gudanar da bincike a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng