An Shiga Tashin Hankali a Neja da Tankar Gas Ta Yi Bindiga, Motoci Sun Kone Kurmus

An Shiga Tashin Hankali a Neja da Tankar Gas Ta Yi Bindiga, Motoci Sun Kone Kurmus

  • Rahoto ya nuna cewa wata tankar gas ta fashe yayin take sauke gas a tashar gas a Sabon Wuse, lamarin ya jawo babbar gobara
  • An ce gobarar ta kona shagunan kayan abinci, motoci da dama da wasu sassa na gidan man fetur da ke kusa da wurin da abin ya faru
  • Sai dai an tabbatar da cewa babu asarar rai, amma an ce Allah ya tseratar da mazauna yankin saboda lamarin ya faru ne da dare

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Rahotanni sun bayyana cewa wani gidan mai ya kama da wuta tare da kona motoci da shagunan kayan abinci a a karamar hukumar Tafa, jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa fashewar ta faru ne yayin da wata tankar gas ke sauke gas a tashar sayar da gas da ke garin Sabon Wuse.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Kano, gobara ta kashe dabbobi 78, ta lalata kayan abinci

Mazauna Sabon Wuse sun fadi yadda tankar gas ta fashe tare da babbaka motoci da shaguna
An shiga fargaba a Neja da wani gidan mai ya kamata da wuta tare da kona motoci.
Asali: Original

Tankar mai ta fashe a jihar Neja

Wani ganau ya shaida wa Daily Trust cewa wutar ta tashi kusan karfe 11 na dare kuma ta dade tana ci kafin masu kashe gobara su isa wajen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin, Abdul Sabon-Wusa, ya ce fashewar tankar ta girgiza unguwannin da ke kewaye, inda mutane suka rika gudun ceton rai daga gidajensu.

Ya kara da cewa wutar ta kai ga wasu sassan wani gidan man fetur da kusa da wurin, inda ta kona shagunan kayan abinci da motoci da dama.

Yadda gidan mai ya kama da wuta a Neja

Abdul Sabon-wuse ya shaidawa manema labarai cewa:

“Mun gode wa Allah babu rai da ya salwanta kuma babu wanda ya ji rauni. Da hakan ya faru da rana, to da labarin ya kasance na daban.
“Idan ka na kallon wutar, za ka ga yadda ta ke tsiri tana tashi sama sosai, wanda karfinta ya sa har ta ake iya gano ta daga dukkanin fadin Sabon Wuse."

Kara karanta wannan

Tankoki 2 makare da fetur sun fashe a wani gidan mai a Adamawa, gobara ta tashi

Mutanen yankin sun yaba da yadda ba a samu asarar rai ba duk da irin girmar gobarar da ta faru.

Tankar mai ta sake fashewa a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ana fargabar cewa mutane hudu sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wata tankar man fetur a garin Kusogbogi, jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa tankar ta kama wuta yayin da take wucewa kusa da wata babbar mota, lamarin da ya haddasa fashewar ta da wata mota.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.