Sallar Layya: Halin da aka Shiga a Najeriya bayan Tchiani Ya Hana Fitar da Dabbobin Nijar

Sallar Layya: Halin da aka Shiga a Najeriya bayan Tchiani Ya Hana Fitar da Dabbobin Nijar

  • Yayin da ake dab da shiga lokacin bikin babbar sallah, ana hasashen tashin farashin dabbobi sakamakon hana fitar da dabbobi daga Jamhuriyar Nijar
  • Nijar ta dauki matakin ne domin daidaita farashin dabbobi a kasarsu kafin bukukuwan Idi, lamarin da zai shafi kasashe makwabta ciki har da Najeriya
  • Masu fatauci a Kano da Jigawa sun fara duba kasashen Kamaru da Chadi don maye gurbin dabbobin layan da ake shigowa da su daga kasar Nijar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Yayin da bikin babbar sallah na bana ke kara karatowa, ‘yan kasuwa da masu sayen dabbobi sun nuna damuwa kan yiwuwar tashin farashin raguna da sauran dabbobi.

Wannan na zuwa ne sakamakon rahotanni da ke nuna karuwar satar dabbobi a Arewa maso Yamma da kuma haramcin fitar da dabbobi daga kasar Nijar da aka sanar a watan Mayu.

Raguna
Ana fargabatar tashin farashin raguna bayan hana shigo da dabbobi daga Nijar. Hoto: Legit
Asali: Original

Daily Trust ta rahoto cewa ma’aikatar kasuwanci ta Nijar ta dauki matakin ne domin tabbatar da wadatuwar dabbobi a cikin gida yayin bukukuwan Sallah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa Nijar ta ce an dauki matakin ne ganin cewa kashi 90 cikin 100 na al’ummar kasar Musulmi ne.

Sallah: Za a yi karancin dabbobi a Najeriya

Ministan Kasuwanci na Nijar, Abdoulaye Seydou, ya bayyana cewa gwamnati ta umarci jami’an tsaro su sanya ido tare da hukunta duk wanda ya karya wannan doka.

Najeriya da Côte d'Ivoire da ke dogaro da shigo da dabbobi daga Nijar za su fi fuskantar tasirin wannan mataki.

Hakan na zuwa ne ganin cewa Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin manyan masu kawo raguna, tunanin da ke tada hankalin ‘yan kasuwa a Najeriya.

A kasuwannin Kano da Jigawa, ‘yan kasuwa sun bayyana damuwarsu kan yiwuwar karancin dabbobi da tashin farashi a lokacin sallah.

Masu fatauci za su koma Kamaru da Chadi

Wani dan kasuwa a kasuwar dabbobi ta Wudil, Malam Abdullahi Abdul ya ce haramcin zai shafi yawan dabbobin da ke shigowa Najeriya daga Nijar.

Malam Abdullahi Abdul ya ce lamarin zai iya haifar da karancin dabbobi da kuma hauhawar farashi.

Rahoton Trust Radio ya ce dan kasuwar ya ce:

"Mun fara tura wakilai zuwa Kamaru da Chadi domin cike gibin da zai iya tasowa. Amma bambancin canjin kudi zai iya sa farashi ya tashi."

Shi ma wani dan kasuwa, Alhaji Bello Guri, ya bukaci jama'a da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa dabbobi sun fara shigowa daga wasu kasashe tun kafin lokaci ya kure.

Ragon sallah
'Yan Najeriya sun fara shigo da dabbobi daga kasashe. Hoto: Legit
Asali: Facebook

Halin da ake ciki a kasuwar Maigatari

A kasuwar dabbobi ta kasa da kasa da ke Maigatari a jihar Jigawa, ‘yan kasuwa sun bayyana damuwa kan yadda haramcin zai kawo cikas ga harkokinsu.

Malam Dauda Babandi Gumel ya ce kasuwar na hada hada a Nguru, Garin Alkali da Dapchi a Yobe, amma tana dogaro da Nijar wajen samun raguna daga Dingas, Magarya Tsira da Matarka.

Ya ce matakin ya katse zirga-zirgar masu sayar da dabbobi daga Najeriya da ke kaiwa har kasuwannin Nijar don sayo raguna a cikin manyan tireloli su kawo su Maigatari.

Legit ta tattauna da Ibrahim Sa'idu

Wani mai sayen dabbobi a jihar Gombe, Ibrahim Saidu ya ce ba lallai hana shigo da raguna daga Nijar ya yi tasiri ba a jihar.

Ibrahim ya ce:

"Yawanci a jihar Gombe ake sayen ragunan da ake amfani da su, saboda haka ba za mu fuskanci wani kalubale sosai ba.
"Sai dai kamar yadda kowa ya sani ne farashin abubuwa sun tashi a Najeriya, saboda haka dole farashin dabbobi ma su tashi."

Nijar ta nemi taimakon Najeriya kan fetur

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin soji ta kasar Nijar ta nemi agajin Najeriya kan matsalar man fetur.

Shugaban gwamnatin sojin Nijar ya nemi taimakon ne bayan da ya samu sabani da wasu kamfanonin mai a kasarsa.

Legit ta rahoto cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da ba Nijar tankunan man fetur domin magance matsalarsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng