Sallah: Bayan Sanata Yari, Ɗan Majalisa Ya Ba Ƴan Mazaba Raguna 300, N250m a Zamfara

Sallah: Bayan Sanata Yari, Ɗan Majalisa Ya Ba Ƴan Mazaba Raguna 300, N250m a Zamfara

  • Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bukukuwan salla, Hon. Aminu Jaji ya gwangwaje ƴan mazaɓarsa a jihar Zamfara
  • Jaji ya raba raguna 300 da makudan kudi har N250m ga shugabannin APC da mambobinsu da sauran jama'a a mazaɓarsa
  • Legit Hausa ta ji ta bakin daya daga cikin wakilan Hon. Aminu Jaji kan gwangwaje ƴan mazabarsa da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Dan Majalisar Tarayya a jihar Zamfara, Hon. Aminu Jaji ya raba raguna 300 saboda bukukuwan sallah.

Jaji ya raba ragunan ne ga mambobin jam'iyyar APC da shugabanninsu da kuma marasa karfi a mazaɓarsa.

Dan Majalisa ya sake raba raguna da makudan kudi ga ƴan mazaɓarsa a Zamfara
Hon. Aminu Jaji ya raba raguna 300 da N250m a Zamfara. Hoto: @Aminu_Jaji.
Asali: Twitter

Zamfara: Hon. Jaji ya yi abin alheri

Kara karanta wannan

Bayan tsige Mamman Ahmadu, Tinubu ya ba tsohon kwamishinan Legas wani babban muƙami

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugabanni kwamitin gudanarwar dan Majalisar, Aliyu Abubakar ya fitar, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aliyu ya ce Hon. Jaji ya kuma raba N250m ga ƴan mazabar da sauran marayu da marasa karfi domin yin bukukuwan sallah.

"Wannan kyautatawa ce ta shekara wanda ya ware domin mambobin APC da sauran jama'a domin yin walwala a sallah."
"Wadanda za su ci gajiyar sun hada da shugabanni jam'iyyar a matakin jiha da kananan hukumomi da unguwanni."
"Sannan sauran sun hada da dattawan jam'iyyar APC da tsofaffin wadanda suka rike mukaman siyasa."

- Abubakar Aliyu

Zamfara: Masu cin gajiyar goron sallah

Sauran masu cin gajiyar sun hada malaman addini da kungiyoyi n APC da mata da mataa da marasa ƙarfi.

Ɗan Majalisar shi ke wakiltar mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara karkashin jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Bayan an koka da nade-nadensa, Tinubu ya ba amininsa mukami a Gwamnatin Tarayya

Legit Hausa ta ji ta bakin daya daga cikin wakilan Hon. Aminu Jaji kan gwangwaje ƴan mazabarsa da ya yi.

Hon. Mansur Khalifa wanda tsohon kwamishina ne a Zamfara ya tabbatar da rabon ɗan Majalisar.

"Ai abin da Hon. Jaji ya raba ba iya mazabarsa kadai ba ne, duk jihar Zamfara ya raba."
"Ya raba fiye da raguna 2,000 a ƙananan hukumomin Zamfara 14 kuma an raba lafiya babu matsala."

-Mansur Khalifa

Kungiya ta yi barazanar kiranye ga Jaji

A wani labarin, kun ji cewa wasu a mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara sun fara shirin kiranye kan ɗan Majalisar Tarayya a yankin, Aminu Sani Jaji.

Jama'ar yankin suka ce sun yi nadamar zaben Jaji shiyasa suke kokarin daukar wannan mataki a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel